Connect with us

LABARAI

Tun Bayan Yakin Biyafara… Nijeriya Na Fuskantar Yanayi Mafi Muni – Sarkin Daura

Published

on

  • Amma Ya Yaba Wa Fadi-tashin Burutai

Dangane da halin da Nijeriya ta tsinci kanta na rashin tsaro musamman a Arewa ta yadda ‘yan bindiga da fashi da masu satar mutane ke cin karensu babu babbaka, Mai Martaba Sarkin Daura, Dakta Umar Farouk Umar (OON), ya ce, babban kalubalen da a ke fuskanta a yau ya zarce na lokacin yakin basasar kasar.
Sarkin ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke tsokaci kan a fadarsa, yayin da Babban Hafsan Sojojin kasan Nijeriya ya kai ziyarar gani-da-ido a yankin na Daura kan halin tabarbarewar tsaro da a ke fama da shi a karshen mako.
Ra’ayin Sarkin na Daura ya zo daidai da abin da kungiyoyi irinsu Ohanaeze Ndigbo, PANDEF da Afenifere na Ibo, Neja-Delta da Yarabawa su ke fada game da halin da a ke ciki.
Sarkin ya bayyana cewa, hanyar kawo karshen wannan musifa da a ke ciki ita ce a dage da addu’o’i da abinda ya dace ta hanyar ajiye bambancin ra’ayi, kamar yadda a ka yi har a ka kawo karshen rikicin Biyafara a baya.
Sai dai kuma Sarkin ya yaba da kokarin da sojoji su ke yi na ganin an samu zaman lafiya a Daura da fadin kasar tun bayan da Janar Tukur Buratai ya shiga ofis a matsayin Babban Hafsan Sojojin kasar. Mai Martaba Umar ya ce ya ji dadin irin aikin da Tukur Buratai ya ke yi, ya bukaci a ba shi goyon-baya.
Shugaban Hafsoshin Sojin ya yi amfani da wannan dama wajen gaida Sarkin Daura, inda ya bayyana ma sa shirin da bataliya ta 171 ta sojojin kasa su ke yi na kawo karshen ta’adin ‘yan bindiga.
Janar Buratai ya roki Mai Martabar da mutanen garin Daura su sa sojojin kasa a addu’a. Ya ce dakarun Nijeriya za su kawo karshen matsalar rashin tsaron nan ba da dadewa ba.
Tukur Yusuf Buratai ya tabbatar wa masarautar mahaifar shugaban kasar Nijeriya cewa sojoji za su zabura da zimmar magance matsalolin tsaro, musamman a yankin na Arewa maso Yamma. Sojan ya ce ya kawo wannan ziyara ce domin duba da ta’adin da ‘yan bindiga su ke yi a jihar Katsina.
“Yanzu sojojin Nijeriya sun fara sauya tsare-tsare a fadin Najeriya, kuma manyan sojojin kasar sun zo jihar ne domin dabbaka umarnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da na magance matsalar rashin tsaro a kasar,” in ji Buratai.
Advertisement

labarai