Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home FASIHAI

Tun Ina Makarantar Firamare Na Ke Da Sha’awar Rubutu – Marubuciya Nafisat Aliyu

by Sulaiman Ibrahim
December 31, 2020
in FASIHAI
5 min read
Marubuciya Nafisat Aliyu
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Assalamu Alaikum. Barkan mu da sake kasancewa da ku a filin ku na FASIHAI. Shafi  da ke zakulo mu ku shahararrun marubuta da mawakan hausa, tare da wakiliyar LEADERSHIP A YAU, SADIYA SIDI SAID, wacce aka fi sani da SIDIYA.

Bakuwar mu ta mako itace NAFISAT MUHAMMAD ALIYU. NAFISAT daya ce daga cikin fitattun marubutan mu na yanar gizo. Ta nishadantar da ku a cikin littafai da dama, daya daga ciki shine Masarautar Narkus. Ga yadda tattaunawar ta kasance.

samndaads

 

Nafisat, masu karatu za su so jin dan takaitaccen tarihinki?

 

Ya aka yi ki ka tsinci kanki a harkar rubutu?

Gaskiya da ma tun ina makarantar firamare ina da sha’awar rubutu, daga baya kuma na zo ina rubuta takaitattun labarai, sai a yanzu kuma da na samu cikakkiyar kwarin gwiwar da ya sa na tsunduma a harkar rubutu, wanda na samu daga Shamsiyya Abdullahi (ummu dilshad), wacce ta kasance marubuciyar yanar gizo.

 

A dunkule mai ki ka fahimta game da rubutun hausa, sannnan menene manufar naki rubutun?

A gaskiya abunda na fahimta game da rubutun hausa shine, wata hanya ce ta isar da sakonni, da ma kokarin gyaran  wasu abubuwa da suke faru a cikin al umma. Manufar rubutuna kuma shine, domin samun damar isar da wasu sakonni masu muhimmanci ga al’umma da ma fadakarwa hadi da nishadantarwa.

 

A gaskiya dai a yanzu ban cika shekara da fara rubutu a yanar gizo ba. Na rubuta littatafai gudu uku.

 

Ko za ki iya lissafowa masu karatu su?

Littafina na farko shine 1. Nida ya mj, sannan 2. Rayuwar bilkisu  sai 3.masarautar narkus.

 

Wanne ne bakandamiyar ki daga ciki?

A gaskiya wanda ya kasance bakandamiyata a ciki shi ne Masarautar Narkus.

 

Me ya sa ki ka fi son wannan littafi, sannan a dunkule wani sako yake dauke da shi?

A gaskiya abun da ya sa nafison wannan littafi shine, yana dauke da abubuwan burgewa wanda suka danganci mulki da ma tsantsar soyayya, hadi da daukaka da addinin musulunci  yayi a wannan littafi. A dungule wannan littafi na nuna daraja da falalar da ke cikin addinin musulunci, da ma kuma tsantsar soyayya dake shiga zuciyoyin wanda suka kasance su ne jarumai a cikin wannan littafi.

 

Toh, a gaskiya ni dai babu wanda ya ba ni shawarar fara rubutu a yanar gizo, na fara ne dan ra’ayin kaina, sai dai bayan na fara na samu kwarin gwiwa sosai wanda shine ya karfafa min gwiwa sosai a harkar rubutuna na yanar gizo, da irin kwarin gwiwar da na ke samu wanda shi ke dada karfafa min gwiwa a koda yaushe.

 

A ganin ki rubutu dace ne da cancanta ko kuwa kowa ma zai iya zama marubuci ko marubuciya?

A gaskiya a ganina rubutu ba cancanta bane, ba kuma dacewa ba, sai dai shi rubutu baiwa ce kawai daga Allah, ta yadda bawai kai ka ke tsarawa kanka cewa za kai rubutu ba koma makamancin hakan, saidai hakan kawai yana zuwa ne bisa baiwa daga Allah da ma tsantsar basira. A gaskiya wannan shi ne kadan daga abunda na fahimta na dangane da rubutu.

Kasancewar an samu ci gaba a duniyar rubutu na wanzuwar kungiyoyi masu zaman kan su, shin ko akwai wata kungiyar da ki ke ciki? Idan akwai masu karatu za su jin sunan kungiyar da manufarta a takaice?

Eh, a gaskiya ina karkashin wata kungiya mai suna ‘intelligent writers association’, wacce fatan  ta a koda yaushe shi ne kawo  sauyi na musamman a cikin duniyar rubutu, musamman bangaren bluebook wato rubutun batsa, wanda yasa mutane da dama ke kallon marubutan yanar gizo duk manufarmu daya. To a gaskiya dai su na iya kokarinsu, domin kawo sauyi a wannan bangare.

 

Me Nafisat ta fi so ta bangaren abinci da abun sha da kuma nau’in sutura?

Nafisat a bangaren abinci ta fi son shinkafa da wake da kayan ganye, abun sha kuma gaskiya na fi son zobo ko kunun aya. Bangaren sutura kuma gaskiya na fi son atamfa.

 

Ko akwai wata shawara da za ki baiwa masu karatu har ma da marubuta ‘yan uwanki?

Shawarar da zan bai wa marubuta ‘yan uwana shi ne, su sani cewa a koda yaushe za su yi rubutu to su tabbata sun yi wanda zai amfanar da al’umma da fadakar da su, bawai rubutu wanda kwata-kwata ba shi da alfanu ga rayuwar dama addinin mu amatsayin mu na musulmai. Mu kasance masu kishin addinin mu da ma abunda zai gurbata mana zuri’a dama mu’amala. Dan haka ina mai rokon alfarma a gurin ‘yan uwana marubuta akan su kasance masu  tsaftace alkalaman su akoda yaushe, sannan su ma masu karatu ina mai basu shawarar su kasance masu sanin abunda za su karanta akoda yaushe wanda ya kasance zai amfanar da su, ba wai wanda zai gurbata musu al’adar su ba har ma da addinin su

 

Wace ce tauraruwarki cikin marubutan yanar gizo da kuma mawallafa?

Tauraruwata a bangaren marubutan yanar gizo ita ce Shamsiyya Abdullahi, wato Ummu Dilshad. A bangaren mawallafa kuma Fauziya D. Sulaiman.

 

Ko akwai albishiri din da ki ke dauke da shi da za ki yiwa masoyanki?

albishir dina ga masoyana shine su cigaba da kasancewa tare dani domin akwai tanadaddun labarai wanda za su yi matukar nishadantar da su dama fadakarwa a cikin wannan sabuwar shekara da za mu shiga insha Allah, sai dai fatan mu kawai ga masoyanmu shi ne su cigaba da yi mana addu’a hadi da fatan alkhairi.

 

Mene ne burinki nan gaba game da rubutunki?

Burina a nan gaba game da rubutu na shine, na yi fice sosai a harkar rubutu wanda zai dinga fadakar da al’umma dama nishadantar da su. Abu na gaba kuma Ina fatan  zama marubuciyar finafinan Hausa dirama siris, wato ‘script writer’ in sha Allah

 

Nafisat, LEADERSHIP A YAU na yi mi ki fatar alkhairi.

To, ma sha Allah. Hakika ina matukar godiya da ma farin cikin kasancewa da daya daga cikin wanda LEADERSHIP ta gayyata a wannan rana, sai dai na ce rabbi yabar zumunci, ya kuma yi ma na jagora. Amin.

SendShareTweetShare
Previous Post

Alamomi 50 Da Ake Gane Mata ‘Yan Madigo

Next Post

Waye Gwani Tsakanin Anthony Joshua Da Tyson Fury?

RelatedPosts

Sharifiya

Kafin Na Tsinci Kaina A Harkar Waka Sai Da Na Fara Rubutu –Mai Sharifiya

by Muhammad
1 week ago
0

Assalamu Alaikum. Barkanmu da sake kasancewa da ku a filinku...

Balannaji

Sha’awa Ce Ta Kawo Ni Fagen Rubutu, Cewar Marubuci Balannaji

by Muhammad
1 month ago
0

Assalamu Alaikum. Barkanmu da sake kasancewa da ku a filinku...

Marubuciya Feedyn Bash

Wasu Bayin Allah Ne Suka Karafafa Min Yin Rubutu – Marubuciya Feedyn Bash

by Sulaiman Ibrahim
2 months ago
0

Assalamu Alaikum. Barkanmu da sake kasancewa da ku a filinku...

Next Post
Anthony Joshua Da Tyson Fury

Waye Gwani Tsakanin Anthony Joshua Da Tyson Fury?

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version