Daga Khalid Idris Doya,
Jami’an tsaron ‘yan sandan shalkwatar Ogun sun samu nasarar cafke wani mutum mai shekaru 49 a duniya, Mista Obong Williams Akpan, biyo bayan da wata diyar cikinsa ta kai rahoton cewa kullum sai ya yi mata fyade tsawon shekaru biyar.
‘Yar mai shekara 12 a duniya ta shaida wa ‘yan sanda cewa mahaifin nata ya fara kwana da ita ne tun tana ‘yar shekara bakwai a duniya ba tare da sonta ba wanda ma hana hawa kanta ne bisa tursasawa da tilasta mata.
‘Yan sanda sun ce, Mista Obong Williams Akpan ya yi ikirarin cewa matarsa ta jima da tsufa kayan alatun jikinta ba su burgeshi ko gamsar masa da sha’awarsa wanda hakan ne ya kaisa ga neman mafitar kwanciya da ‘yarsa karama domin biyan bukatarsa ta sha’awa.
Jami’an sun kama shi ne a ranar 2 ga watan Maris lokacin da yarinyar ta kai kara ga caji ofis din ‘yan sanda na Itele Ota.
Karamar yarinyar ta shaida wa ‘yan sanda cewar mahaifinya ta shafe shekaru biyar na saduwa da iya ba tare da shirin dainawa ko tausaya mata ba, don haka ne kawai ta yanke shawarar kai kararsa ga ‘yan sanda domin ceto daga wannan halin da mahaifinta ya jefata ciki.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Edward Ajogun, ya umarci a maida kes din zuwa sashin kula da harkokin dafa wa iyali na shalkwatar da ke Ota domin zurfafa bincike da shirin gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu domin fuskantar shari’a daidai da laifinsa.
Sannan, ya umarci a dauki yarinyar da tsautsayin ya rutsa da ita zuwa babban asibiti domin binciken matakin lafiyarta da mata magani domin ceto rayuwarta daga matsalolin da ka iya fuskantarta.