Tun Sani Dankwairo Ba A Sake Samun Kamar Lil Ameer A Kasar Hausa Ba — Farfesa Abdalla

Marigayi LIL AMEER fasihin karamin yaro ne wanda ya taso da matukar basira da fice a harkar waka, wacce ta shafe yawancin basirar wacce a ka saba gani a kasar Hausa ga kananan mawaka, to amma ashe ba mai tsawon rai ba ne; Lil ya yi rasuwa ta bakatatan a ranar 14 ga Satumba, 2017, ya na shekaru 14 kacal; lamarin da ya gigita al’ummar kasar Hausa, musamman mata da matasa.

FARFESA ABDALLA UBA ADAMU ba boyayye ba ne a Arewacin Nijeriya da ma kasashen waje, domin ya kasance tamkar rumbun dakin karatu (library) mafi girma da a ka taba yi a kasar Hausa, musamman a fannin nazari da binciken nishadi a hausance. Kafinrasuwar Lil Ameer a na kallon Farfesa Abdalla a matsayin wanda shi ne mujazar tallata wannan fasihin yaro, domin Farfesa Adamu ba boyayye ba ne wajen taimaka wa matasa masu fasaha irin Ameer.

Editanmu NASIR S. GWANGWAZO ya tuntubi shehin malamin jami’ar, wanda kuma shi ne mataimakin shugaban jami’a mai cikakken iko ta Nijeriya da ke yanar gizo (NOUN), don jin ta bakinsa kan wannan babbar asara da kasar Hausa ta tafka. Duk da irin dimbin hidindimun da ke gaban Farfesa Abdalla bai yi kasa a gwiwa ba wajen bayar da wasu cikakkun bayanai, wadanda ba a taba jin su a kan rayuwar Lil Ameer ba. Babban abin mamaki shi ne har Lil ya rasu ba su taba haduwa ido-da-ido da Farfesa ba, duk kuwa da irin dimbin gudunmawar da ya ke bai wa rayuwar yaron, wanda hakan ke nuni da irin sadaukarwar Malam Abdalla ga cigaban harshen Hausa. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Mai girma Farfesa, shin mene ne cikakken sunan wannan mashahurin yaron mawaki da ya rasu, kuma da wane suna ya ke amfani a fagen waka?

Cikakken sunansa Amir Hassan Isa Bello Dambatta. Amma an fi sanin sa da ‘Lil A’,  sunan da shi kansa ya lakaba wa kansa ko kuma ‘Lil Ameer’ (mai nufin Amir dan karami), a  matsayin sunansa na mawaki, kamar yadda sauran manyan mawakan Rap na Amurka ke yi, misali Dwayne Michael Carter, Jr, wanda a ka fi sani da Lil’ Wayne.

 

Ta ya ya labarin rasuwarsa ya riske ka, kuma mene ne sanadin rasuwarsa?

Hassan M. Sheriff na Radio Freedom shi ya fara kira na ranar da abin ya faru, watau Alhamis 14 ga Satumba da yamma ya sanar da ne cewa ‘Allah Ya yi wa dan gidan ka rasuwa’. Na ce‘ai suna da yawa, wannene daga cikin su?’ Ya ce ‘Lil Ameer’. Wannan sanarwa ta girgiza ni matuka, domin ranar ma kasa ci gaba na yin da ’yan aikace-aikacen da na ke yi na rubutu, domin sai na ji duk na rasa ma abin da zan yi, Ina cike da dimautuwa. A na ce ma sa ‘Dan gidan Baba Furof’, saboda yadda na ke tallata shi a duniya da kuma begen wakokinsa. Na so in hadu da shi, domin ganin yadda zan taimaka wajen bunkasa sha’awar sa ta waka, tare da la’akari da cewa shi dan sakandare ne, saboda haka akwai bukatar ya mayar da hankali sosai wajen karatun sa. Allahu Akbar. Allah Ya jikan sa da Rahama. Allah Ya ba mu dangana da hakurin rashin wannan yaro fasihi. Mun buga ta’azziyar sa a http://www.afropop.org/39156/lil-ameer-a-nigerian-rap-prodigy-leabes-us-too-soon/

Daga bayanin da ya zo daga baya, sun yi hatsari ne a kan babur. Shi dai an goyo shi ne a kan babur din, sai wani dan Adaidaita Sahu, ya yi musu ganganci wajen shige su, wanda haka ta tankada babur din na su karkashin wata DAF mai tahowa, wacce ta take babur din tare da Ameer din, ta  yi sanadiyyar rasuwar sa. Shi mai tuka babur din ya rayu amma ya ji rauni sosai. Dan Adaidaita Sahun da aka ce ya janyo hatsarin bai tsaya ba, guduwa ya yi.

 

Mene ne asalinsa da tarihinsa?

An haife shi 22 ga Mayu 2003, ya kuma rasu 14 ga Satumba 2017. Ya rasu ya na da shekaru 14 da watanni uku da rabi kenan. Mutumin Dambatta ne a Kano, amma a Tarauni da ke cikin birnin Kano su ke da zama.

 

Wacce basira ka gani a tattare da shi har ka janyo shi a jikinka?

Abin mamakin shi ne ba mu taba haduwa da shi ba, kamar yadda na gaya maka dazu, to amma mun san juna kuma muna magana ta waya. A lokacin da na gayyaci wadansu Amurkawa daga www.afropop.org su zo su yi shiri na musamman a kan Hausa Rap a farkon Fabairu 2017, Ameer na daya daga cikin mawakan da na ce lallai sai sun yi hira da shi saboda tallata shi a duniya.

 

A ganinka, me ya sa rasuwarsa ta dauki hankalin jama’a?

Dalilai guda biyu. Na farko karancin shekarun sa – mutuwar yara razanawa ce da ita fiye da mutuwar manya. Na biyu basirar sa. A dandankanin lokaci Allah Ya sa sunan sa ya bazu ko’ina, ta yadda sai gayyatar sa a ke yi ya zo ya yi wasa a garuruwa da dama.

 

Ko Malam ya san yadda dangantakar yaron ta ke da mahaifiyarsa?

Dangantakar sa da mahaifiyar sa ba za ta misalu ba, don shi ne ma wanda ta fi shaduwa da shi a cikin ’ya’yanta.

 

Su nawa ne a dakinsu da gidansu, kuma da na nawa ne shi?

Su shida ne a dakinsu, amman shine na uku.

 

A wane hali yanzu iyayensa da ’yan uwansa ke ciki a dalilin rasuwar?

Su na cikin dimautuwa da damuwa, kamar yadda kowacce mutuwa ke kawo wa, ballantana ta dan karamin yaro kuma ba zato ba tsammani.

 

Shin ya na taimakon iyayensa da abinda ya ke samu daga waka, kafin rasuwarsa?

Ai yanzu ya fara, domin ko faifan farko ma bai saki ba tukunna, duk da ya yi wakoki kamar 20. Ya na kan gwaji ne na wakokinsa da kuma karbuwarsu, wanda dama sai an yi haka sosai sannan a saki CD na wakokin da suka fi karduwa. Saboda haka kudin ba su fara samuwa sosai ba, amman dai ya na da tausayin mahaifiyarsa da ’yan uwansa.

Sannan mahaifiyar sa ita ce ta fara zama manaja din sa kafin Abba Usman (Abba PA) ya karbi ragamar abin. Kuma a gaskiya ta kashe kudade da dama a kan harkarsa kafin Allah Ya yi ma sa rasuwa.

 

Shin ko Malam ya san babban burin yaron, kafin ya rasu?

Burinsa ya zama matukin jirgin sama, watau Pilot, duk da cewa ya na sha’awar waka.

 

Wacce asara ka ke ganin al’umma ta yi a dalilin rasuwarsa da ma matasa masu basira irinsa?

Babbar asarar ita ce rashin yaro mai kananan shekaru mai kuma fasaharsa da kwarewarsa wajen sarrafa waka. Tun bayan mutuwar Alhaji Sani Zakin Murya na Dankwairo, ba na jin an samu wani karamin yaro da ya kama kafar Ameer wajen sarrafa waka da kuma rashin nuna tsoron barazanar jama’a in ya hau dandali don yi waka. Shigowarsa cikin sana’ar waka ta rufe wani gidi na nishadin kananan yara a kasar Hausa, wanda kuma kamar yadda jama’a da dama za su iya sani, wadansu daga cikin mashahuran mawakan duniya sun fara ne tun su na kananan yara. Babban misali shi ne Marigayi Michael Jackson wanda ya fara waka ne tun ya na dan shekara biyar.

Haka ma Kris Kross, yara guda biyu, Chris “Mac Daddy” Kelly da Chris “Daddy Mac” Smith, wadanda su ka shahara da wakar Rap mai suna ‘Jump Jump’ sun yi suna ne tun su na ’yan shekaru 12.

A yanzu haka, wannan matsayin ya koma kan Dan Bello Ibrahim (Billy-O), Hani Bello Ibrahim, wanda bai wuce shekaru bakwai ba, kuma babban abokin Marigayi Ameer ne (har ma waKar ta’aziyya Hani ya yi wa Ameer) na nan a raye. Da fatan zai maye gurbin Ameer din.

 

Akwai masu ra’ayin cewa, rasuwar yaron nan ta fi alheri, saboda gudun kada ya zama hatsabibi, idan da ya yi tsawon rai. Me Malam zai ce kan hakan?

Wannan ba daidai ba ne, domin duk Musulmin duniya zai yi wa rasuwar wani Musulmin addu’a ne. Kamata ya yi masu wannan ra’ayin su ma su yi fatan mutuwa yanzu-yanzu, domin babu tabbacin za su dare duniyar da imanin da su ke ganin su na da shi. Saboda haka yaya za su yi hasashen makomar wani?

Sannan kuma Ameer da sani da kuma albarkacin iyayensa ya shiga sana’ar waka – ta wannan ma ai ya samu kariya duniya da lahira daga sharrin shaidan da rundunarsa. Bayan haka, mu da mu ke mara masa baya, ta kowacce hanya, ai mun dauke shi tamkar dan da mu ka haifa, kuma da namu ’ya’yan, wadansu su na waka (kamar dan Billy-O da na yi magana). Ta dada za mu kyale ya lalace bayan amana ya ke a wurinmu? Wannan ba wani abu ba ne illa dyashi da hassada, saboda yaron ya sami daukaka saboda basirar da Allah Ya yi ma sa.

 

Malam, kai kanka da a ke ganin ka yi fice a sha’anin hadaka harshen Hausa, wasu na ganin cewa, ka na rusa yaren da al’adunsa, saboda taimakawa irin wadannan yara masu wakar gambarar zamani (wato hip-hop) da ka ke yi. Me za ka ce kan hakan?

Bari in kawar da wata mummunar fassara tun kafin a yi nisa. Hiphop da Rap ba gambara ba ne. Ko kadan. Wanda duk ya ke fadin haka, to ko da ya san gambara, bai san Hip Hop ba. Jigon gambara akasari batsa, zambo, zolaya, shakiyanci, ban dariya da sauransu. Ko kadan wadannan ba sa cikin abin da Rapawa ke rerawa, takamaimai ma na mu na kasar Hausa.

Hip Hop salo ne na rayuwar matasa ta shigar su ta tufafi. Rap salo ne na wakar matasa, kuma duk wadannan daga Amurka a ka samo asalin sigarsu ta yanzu. Mutum zai iya zama mawakin Rap, amma ba dan Hip Hop ba (misali DMD), kuma ba duk masu ra’ayin Hip Hop ne ke wakar ba. Rap salo ne na harbo furuci a jere, domin nuna gwanintar jera kalmomi su dace da jigon wakar, wanda mu a nan kasar Hausa, akasari a kan ilimi ne, rayuwar duniya, nasiha, da kuma kamfama kai, watau zuga kai.

A kasar Hausa akwai masu Rap tun kafin na zamani ya shigo. Wadannan sun hada da Bagobiri Sullutu da kuma Madawakin Maganana Sarkin Zazzau. A Hausance, wadannan mawakan ba za a kira su ’yan gambara ba. Na ke jin danganta Rap da gambara ya samo asali tun lokacin da Billy-O ya yi wani chalikanci a wakarsa ta ‘Ban Tubani’. Wadanda ba su san me a ke nufi da Rap ba sai su ka dauka ai indai irin yadda Billy O ke yi ne, to gambara ce, wanda haka kuma babban kuskure ne, domin ba su yi bincike sun gane me a ke nufi da Hip hop ba.

Sannan duk wanda ka ga ya lalace, to da ma can lalatacce ne, babu ruwan hanyoyin sadarwa da lalacewarsa. An sha tafka wannan muhawarar. Su masu nishadin hululu gani su ke Ina yi mu su hassada (baran ma ’yan fim) in na janyo hankali a kan al’adu; su kuma mutanen gari gani su ke Ina goyon bayan rusa al’ada. Kullum a wannan tsaka mai wuyar na ke. Har yanzu ba na jin akwai wani mai sana’ar nishadin Hausa guda daya tak da ya taba zama ya karanta abubuwan da na ke rubutawa a kan sana’ar, kuma duk na saka su kyauta a gani a www.auadamu.com.

Na sha fadar cewa ni aiki na, nazari, ba yanke hukunci ba. Duk abin da mutum ya yi zan nazarce shi, ko mai kyau ne ko marar kyau ne – kuma ba zan nuna kyau ko akasin haka ba a abin da mutum ya ke yi, saboda haka ingantancen nazari ya gada: dole manazarci ya cire kansa daga cikin nazarin, ya bayar da bayanin da ya gani bisa doron manhajar tubulin famihta (watau theoretical framework).

 

Shin ya ka ke hasashen zai zama makomar wakokin da a ka fi sani, kafin na gambarar Hausa nan gaba, idan wannan hip-hop ya yi cigaba da bunkasa?

Wadanne ne ‘a ka fi sani’? Ka na nufin na gargajiya? Babu wani yunkurin da mu ke yi na raya su. Kullum sanannun dai su a ke ta juyawa – Shata, Dankwaro, Danmaraya, Sani Sabulu, Dandawo da sauransu. Wadannan ingantattun mawaka ne. Amma wane yunkuri a ke yi domin samar da matasa mawaka irinsu? Ni kaina na fitar da kudi na saki album na wakokin Nasiru Garba Supa, watau dan Marigayi Alhaji Garba Supa, kuma tare da Nasiru mu ka shiga sutudiyo mu ka yi sati guda mu na daukar wakokin, a ka tace a ka bi duk ka’idojin sakin album, a ka sake shi. Amma bai yi kasuwa ba. A Turai, za ka ga a na raya na da, da kuma na yanzu. Misali, yau shekarar Ludwig bon Beethoben, mai rubuta kidan classical, kuma mutumin Bonn, Jamus, 190 da rasuwa. Amma har yanzu a na raya kidansa, kuma wannan bai gushe sababbin makakan classical kamar su Dobrinka Tabakoba, Missy Mazzoli, Judd Greenstein da Ann Cleare da sauransu. Rap dai ya iso, kuma zai rayu. Kazalika kidan gargajiya – in halin-ko-in-kula bai kashe shi ba, domin daya bayan daya, duk wadanda a ka sani sun riga mu gidan gaskiya. In ba a samu madadinsu ba, to wata rana shi ma kidan zan tsaya cak.

 

Mun gode. Allah Ya saka da alheri. Bissalam!

Madalla.

Exit mobile version