Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home MAKALAR YAU

Tuna Baya Shi Ne Roko

by Tayo Adelaja
September 15, 2017
in MAKALAR YAU
6 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Al-Amin Ciroma   08033225331 (TES Kawai )   ciroma14@yahoo.com       

 Idan aka yi la’akari da halin da Nijeriya ta tsinci kanta a ciki, kama daga matsin tattalin arziki, da makuniyar siyasar kasar a yanzu da ke cike da rashin tabbaci da munafunce-munafunce, hada da yadda kallo ya fara komawa sama, a dadai lokacin da aka soma harin zabukan 2019 da kuma uwa uba cin hanci da rashawa da ke neman zame mana kadangaren bakin tulu, shakka babu kowa zai fahimci cewa Nijeriya na bukatar agaji ta kowane fanni.

Kafin wannan lokacin, dukkan zantuka suna tafiya ne kan salon rashin lafiyar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, inda har aka rika samun wasu ‘yan ba ni, na iya suka fara shige da fice. A cikin hakan ne kuwa har ila yau, aka sami wasu wadanda ke rajin dawowa da bakin tarihin da Nijeriya ta tsallake tun daga ranar 6 ga Yulin 1967 zuwa 15 ga Janairun 1970, wato zancen yakin basasa da ikirarin sake dawowa da batun Jamhuriyar Biyafara. Saninmu cewa ita dai haramtacciyar Jamhuriyar Biyafara dai kamar yadda na ambata, ya riga ya zama tarihi, amma duk da haka ba a rasa samun wasu tsagera da suka yi amfani da damar rashin lafiyar shugaban kasa wajen bayyana maitarsu ba.

Duk mai hankali da hangen nesa zai fada maka cewa a yanzu ne ‘yan Nijeriya, musamman ma ‘yan Arewa ke bukatar yi wa kansu karatun-ta-natsu, fiye ma da yadda suka yi a zabukan 2015. Sabili da yadda a yanzu fararen ‘Kuraye’ suka fito haikan da karfinsu don su yi farautar namun daji, ganin cewa ‘Zaki’ ya fara tunanin komawa cikin kogo!

Tabbas, dukkaninmu mun san yadda Allah Ya albarkaci kasar nan da dattawa masu kishinta, wadanda a kullum tunaninsu bai fi a shimfida adalci da ci gaba mai amfani ga kasa ba. A cikin irin wadannan dattawan, wasu sun dan taba a baya, watakila ba su sami cikakken ikon yi wa Nijeriya wani abu ba. Amma a yanzu suna ganin akwai wata dama da za su iya dawowa da karfinsu, don yi wa kasarsu aiki tukuru. Wasu kuwa sabbin jini ne, suna tunanin lokaci ya yi da za yi wa manya da shekarunsu ya ja, da kuma marasa lafiya addu’ar fatan alheri tare da komawa gefe, su ba su waje, su ma su gwada tasu bajintar.

A farkon makon jiya, farfajiyar siyasar kasar ta cika da batutuwa da dama, inda wata minista ta fito ta dan nuna ra’ayinta ga wani dan takara. Zancenta ya kara fito waccan maganar da na fadi a sama cewa; ‘yan Nijeriya na bukatar yi wa kansu karatun-ta-natsu fiye da yadda suka yi a shekarar 2015!

Idan har ‘yan Arewa ba su fahimci logar girmama ra’ayin juna ba, kuma ba su fahimci lokaci ya yi da za a bar kowa ya baje hajarsa faifai ba, ko shakka babu, za mu wayi gari, mulkin da a yanzu muke tutiya da shi a yanzu,  ya sulale daga hannayenmu, ya koma wani yankin na daban, kamar yadda ya faru a shekarar 2011.

Duk da irin wannan kumajin namu na ganin Nijeriya ta wanzu a hannayen masu adalci, zai fi dacewa mu waiwaya baya, sannan mu gano inda matsalar ta samo asali. Wata rana a filin jirgi, na gamu da wani mutum dan asalin kasar Gambiya.

Da yake tafiya ce ta hada mu, ba wai sani na sosai na yi masa ba. Illa a lokacin tattaunawa na ji shi yana ta muzantawa tare da korafe-korafen al’amuran siyasar Nijeriya, har ma ya yi kokarin hada kasarsu da Nijeriya. Ba shakka magangnunsa bisa saiti suke, saboda mu ne da kanmu muka zubar da mutuncin kasar tamu a idanun duniya.

Na ji zafin maganar da mutumin ya yi kwarai da gaske, domin kuwa babu dadi ko na miskala-zarratin, har ya rika fadin maganganu marasa tushe ga kasarka. Babban abin da ma ya ba ni takaici shi ne, idan wani zai raina Nijeriya, to bai kamata dai a ce daga kananan kasashen irin su Gambiya ba!

Wane matsayi kasar Gambiya ke da ita, idan ka kwatantata da Jihar Kano? Na daya dai ba ta kai girman rabin Jihar Kano ba! Kwata-kwata ‘yan kasar ba su haura milyan biyu ba kammar yadda kididdikar shekarar 2013 ta nuna. Sannan ta sami ‘yancin kanta ne shekaru biyar bayan Nijeriya na cin gashin kanta. Amma sai ga shi wani ya fito daga kasar, har zai iya shigowa yana daga kafadarsa tare kyamar Nijeriya! Duk da haushin da na ji, a gefe guda kuma na san gaskiya ya fadi. Duk mai hankali zai ji tsoron halayen wasunmu a nan kasar.

Idan ka dan Waiwaiya baya kadan, tilas ka zubar wa Nijeriya da hawaye. Misali, a shekarar 1974 kadai idan ka duba, kasar nan ta kasance tamkar ‘Aljannar’ duniya saboda komai na tafiya daidai wa daida. Tarihi ya tabbatar da irin kyawawan halayenmu a wannan kasar. Duk bakon da ya shigo Nijeriya, shakka babu da hawaye yake barinta, sannan zai rika Allah-Allah ya sami damar dawowa cikin kankanin lokaci. ‘Yan Nijeriya sun yi fice wajen girmama baki, bin doka da oda. Hatta titunanmu a lokacin, mutum zai iya takawa tun daga kofar gidansa har ya je kasuwa ya dawo cikin jin dadi da tsari gami da yanayi mai kyau.

Ababen hawa na tafiya cikin tsari, masu tafiya a kasa suna tafe cikin aminci, babu kyamar komai don an tsabtace ko’ina,  za ka iske yara suna girmama manya, dattawa suna yi wa al’umma baki daya addu’o’i, zukatan ‘yan kasuwa da sauran masu saye da sayarwa cike da adalci da amana.

Abin takaici, sannu a hankali abubuwa suka rika sauyawa tamkar an shafe wadancan ‘yan Nijeriyan ne aka halitto wadansu daban! Wannan ta sa na ce, ina ma da Allah zai aiko Mala’ika ya debe duk jinanenmu na son abin duniya, na takamar banza da wofi, na tsageranci, na karya doka da oda, na cin hanci da rashawa, na zalunci da cin amana, sannan ya dura mana jini mai kyau mai cike amana!

Shin ina mafita? Zai yiwu a gyara kasar nan? Idan har zai yiwun, wane ne zai gyara ta? Ta yaya za mu dawo da martabar Nijeriya, wacce a da ake alfahari da ita a duk duniya? Ta yaya za mu kara inganta mutuncin shugabanni da ‘yan majalisunmu? Wane abin kunya ne ya fi wanda muke gani a yau? Kasar Nijeriya da aka fi saninta da rikon addini da amana, amma sai ga shi a shekarun baya, Ambasadan kasar Amurka James Entwistle ya fito ya zargi ‘yan majalisunmu da neman yin badala da mata, kaico!

Ko kadan Ambasadan Amurkan bai yi laifi ba, domin ya samu damar yin hakan ne. Babban takaici kuma shi ne, hatta iyalan ‘yan majalisan da ake zargi da neman yin badala da matan a Amurka, sai da suka fito suna Allah wadai da Mr. Entwistle kan cewa sharri ake yi wa ‘yan majalisar. Sai dai tambayar da ba ta da amsa a nan ita ce; me ya sa manuniyar ba ta nuna kowa ba sai su?

Na sha fadi a wannan shafin cewa canjin nan da ‘yan Nijeriya suka zaba gami da alkawuran da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi wa al’umma tun lokacin yakin neman zabe, ba abu ne da zai aikata shi kadai ba.

Matukar dai masu kishin kasar suna muradin gyaruwarta, tilas ne a dawo a yi wa kai fada, a nemi gaskiya da masu ita a karfafa musu gwiwa. Shugabannin da suke bisa turbar gaskiya, a bi su daidai yadda ya kamata.

A dukkan ma’aunai, ba za mu yi laifi ba idan muka ce rashin da’a a yau, ya zama daya daga cikin manyan dabi’un ‘yan Nijeriya a yau. Gidajenmu, makarantu, ma’aikatun gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu, asibitoci, hatta wuraren ibada a kasar sun zama abin tinkaho da rashin da’a.

Wadanda suka rayu a zamanin mulkin soja da Janar Buhari ya rika saka wando daya da masu karya doka, hakika ya gani a zahiri cewa an yi gagarumin aiki wajen tababtar da dan Nijeriya ya zama mutumin kirki, wanda hatta a gidajenmu babu wanda zai so ya tara bola, don gudun kada doka ta yi aiki a kansa. Duk kuwa da sanin cewa zamanin soja da dimokuradiyya ba daya ba ne, amma akwai hanyoyi da dama da za a sake bullo da wannan shirin a dimokuradiyyance don gyara wannan kasa, wadda a kullum nake fadin babu kamar ta a duniya. Babu abin da muka rasa a Nijeriya, Allah Mai Girma da Iko, ya wadatar da mu da komai, kama daga ma’adinai, albarkatun ruwa, iska mai kyau, filayen noma, wadatacciyar kasa mai ni’ima, al’umma masu yawa, masu lafiya da kuma babban abin sha’awa wasu hadakar jama’a daban-daban.

Ashe kenan ya kamata shugaban kasa, ya mayar da hankalinsa wajen ganin ya sake dawowa doka da oda a Nijeriya. Ko wannan ne kadai Buhari zai sa a gaba har a kai karshe, na tabbatar babu wani mai hangen nesa a kasar nan da zai ce shugaban kasa bai tsinana komai ba a shekaru hudun da zai yi a gadon mulkin Nijeriya.

Matukar ba a daidaita al’ummar Nijeriya wajen bin doka da oda ba, a gaskiya tafiyar za ta kara yi mana nisa, siyasar 2019 dai ta fara kunno kai. Allah Ya kara hada kanmu, don fuskantar manyan kalubalen da ke tafe, ameen!

SendShareTweetShare
Previous Post

BANGON FARKO

Next Post

Yayin Da Dan Majalisar Kano Ya Maka Bokan Siyasa A Kotu

RelatedPosts

Deby

Mutuwar Shugaba Idris Deby: Ko Shugabannin Afirka Za Su Darasi?

by Muhammad
4 hours ago
0

Tare da El-Zaharadeen Umar,  A jiya talata labarin rasuwar shugaban...

Talaka

Allah Sarki Talaka!

by Muhammad
2 days ago
0

Kai! gaskiya ana fama da wani abu wai shi kirkirarren...

Ramadan

Ramadan Kareem Alhajin Allah 

by Muhammad
3 days ago
0

Yau a kofar gidan Alhajin Allah zai kwankwasa kofa da...

Next Post

Yayin Da Dan Majalisar Kano Ya Maka Bokan Siyasa A Kotu

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version