Tunanin Mai Da Muradun Kasa a Gaban Kome Shi Ke Karawa ‘Yan Sama Jannatin Kasar Sin Karfin Gwiwa A Ayyukansu

Daga Amina Xu
Yau Laraba da safe, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya zanta da ‘yan sama jannati dake cikin kumbo Shenzhou-12 da kasar ta yi nasarar harba wa kwanan baya. Ya ce, wadannan ‘yan sama jannati uku sun zama abin koyi a sha’anin binciken sararin samaniya.
Ran 17 ga watan, aka harba kumbon Shenzhou-12 dauke da ‘yan sama jannati uku zuwa tashar binciken sararin samaniyan Sin mai sunan “Tianhe”. Bana ta cika shekaru 18 da zuwan ‘yan sama jannati na kasar Sin sararin samaniya, har ma aka fitar da kalmar “Taikonaut” da ke da ma’anar ‘yan sama jannati na kasar Sin, inda aka hada Kalmar Sinanci da Turanci, don yabawa gudunmawar da ‘yan sama jannatin kasar suka bayar.
Yau za mu gabatar muku wasu labarai dangane da wadannan kwararrun ‘yan saman jannati na kasar Sin, don ganin dalilin da ya sa suka samu irin wadannan ci gaba mai armashi.
Nie Haisheng, daya daga cikin ‘yan sama jannati uku dake kumbon Shenzhou-12 a wannan karo, ya kuma taba shiga aikin Shenzhou-6 da aka aiwatar a watan Oktoba na shekarar 2005, a waccan lokaci, kafin ya shiga wannan aiki, ya koma gida don gai da mahaifiyarsa wadda ba ta da lafiya, har ba ta iya yin magana. Dan uwansa ya gaya masa cewa: Ka je aikinka, zan kula da mahaifiyarmu, kada ka damuwa.
Kishin kasa da bautawa iyaye, nagartattun al’adun gargajiyar kasar Sin ne, wannan yana nufin kulawa da tsoffi a gida da nuna himma da gwazo a wajen aiki, don sauke nauyin dake wuyan kowa ne mutum na ciyar da bunkasuwar kasa gaba. Wannan ra’ayi ya samu amincewa sosai a zukatan Sinawa, wanda ya sa kaimin farfadowar al’ummar Sinawa da ci gaban kasar baki daya.
A watan Satumba na shekarar 2008, ‘yan sama jannati Zhai Zhigang da Liu Boming da kuma Jing Haipeng da ke cikin kumbon Shenzhou-7 sun yi shirin aiwatar da aikin fitowa daga kumbo a sararin samaniya a karo na farko, kuma a lokacin an ga alamar tashin gobara da na’urar sa ido ta nuna, amma bayan sun tabbatar da babu wata matsala bayan cikakken bincike, jagoran wannan aiki Zhai Zhigang ya yanke shawara cewa: fita. Daga baya an ga cewa, na’urar ta nuna alama saboda ba ta saba da yanayin sararin samaniya ba. A yayin wani taron da aka yi bayan sun dawo doron kasa, an yi musu tambaya cewa, a waccan lokaci ko sun nuna damuwa cewa ba za su koma doron duniya ba ko a’a? Liu Boming ya amsa cewa, “jam’iyyar JKS da kasarmu ne suka dora mana wannan nauyi, ba za mu ja da baya ba ko kadan, ko da ma za mu sadaukar da rayukanmu, sai mu kammala aikinmu”.
Mayar da muradun kasa a gaban kome, shi ke karfafa zukatan Sinawa. A watan Oktoban shekarar 2013, kumbon Shenzhou-10 da ke dauke da wata ‘yar sama jannati mai suna Wang Yaping ya shafe kwanaki 15 yana tafiya a cikin sararin samaniya, a yayin da take aiwatar da wannan aiki, iyayenta sun nuna damuwa sosai, bayan da Wang Yaping ta dawo doron duniya, ta tambaye su cewa, ko za su yarda ta sake kama irin aiki a gaba? Mahaifinta ya amsa cewa, “babu shakka, ban da kasancewarki diyyarmu, ke kuma ‘yar sama jannati ce na kasar, idan kasarmu na bukatar ki sake kama wannan aiki, to kamata ya yi ki je ki yi, mu kuma za mu yi miki goyon baya”.
Yang Liwei, shi ne mutum na farko da ya je sararin samaniya a kasar Sin, ya kuma bayyana cewa, wannan shi ne mafarkin ‘yan sama jannatin Sin da ma burin kasar gaba daya, burinsu shi ne raya karfin kasar Sin a fannin binciken sararin samaniya.
A duk lokacin da aka ziyarci cibiyar binciken sararin samaniya, za a fara ne da ganin wata jimla: Muradun kasa a gaban kome. Wannan ya zama daidaiton ra’ayi na dukkan al’ummar Sinawa, dalilin da ya sa hakan shi ne, jama’a na amincewa da al’ummarsu kuma suna alfahari da kasarsu tare da kyakkyawar fata ga makomarsu.
Tun kafuwar rukunin ‘yan sama jannati a shekarar 1998, Zhai Zhigang wanda ya zama daya daga mambobin rukuni na farko ya ce, tun lokacin da suka zama mambobin rukunin, wadannan ‘yan sama jannati sun fahimci cewa, wannan ba aiki ne kawai ba, tamkar wani nauyi ne dake wuyansu da kasar da jama’arta suka dora musu.
Muradun kasa da jama’a a gaban kome, shi ne tunanin dake zukatansu, wannan ya sa suka kudiri anniyyar ciyar da sha’anin binciken sararin samaniya da sauran sha’anoni gaba. (Amina Xu)
Exit mobile version