Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home MAKALAR YAU

Tunasarwa Game Da Matsalar Daba A Siyasa (II)

by Tayo Adelaja
September 18, 2017
in MAKALAR YAU
5 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Dakta Sa’idu Dukawa Malami ne a Jami’ar Bayero, da ke Kano, drahmadsaid@yahoo.com

ME YA HAIFAR DA SIYASAR DABA?

samndaads
  1. Yadda al’umma ta bai wa kudi muhimmanci;
  2. Sai kowa ya dukufa wajen neman kudi;
  3. Aka maida siyasa sana’ar da ta fi kowace sana’a samun kudi;
  4. Ake yashe asusun gwamnati don a sayi mutunci wajen jama’a;
  5. Sai ayyukan hukuma suka tabarbare;
  6. Ya zamo babu makarantun da za su wadaci al’umma, baya ga rashin ingancin karatu;
  7. Kuma babu aikin yi idan aka fita daga makaranta, tunda ‘yansiyasa da jama’arsu sun rabe kudin;
  8. Sauran jama’a suka bazama neman kudi;
  9. Aka yi watsi da tarbiyyar yara, suke shiga uwa duniya babu kyakkyawan shiri sai dogon buri;
  10. Idan kudi sun samu a kashe su ta hanyar wofi, idan ba su samu ba a shiga shaye-shaye;
  11. Kungiyoyin asiri a makarantu suka bullo suna masu bata matasa wajen tabarar al’amura;
  12. Halayyar masu mulki ta son a cika binsu da doguwar tawaga da jiniya tana sa wa su rika biyan matasa don a rika binsu; baya da koyi da wasu (kamar ‘yanachaba) kan yi da tafiyar tawaga irin ta shugabanni;

ILLOLIN DABA A SIYASA

Mai yin daba sh ine farkon mai cutuwa da ita: ta cutar da lafiyarsa, da hankalinsa, da makomarsa; ya rasa ilimi; ya rasa aikin yi; ya rasa kuddi; ya kasa aure; ya dada dulmiya cikin shaye-shaye.

Daga nan sai makwabta wajen cutuwa: ga fargaba ko tsoron abin da dandaba zai iya yi; ga shakar hayakin kayan maye wanda likitoci suka ce ya fi cutarwa a kan sha kai-tsaye; ga barazana ga tarbiyyar yaran unguwa; ga haduwa da ‘yan sace-sace.

Su kansu ‘yansiyasa suna gamuwa da tasu cutuwar: na gwamnati su kasa zaman ofis, su kasa kulla abin kirki, su dawwama cikin tsoron sharrin ‘yandaba – nasu da na wasunsu; ‘yanhamayya su yi asarar abin da suka kashe a kan ‘yandaba kafin zabe.

Gwamnati kanta tana cutuwa: ta kashe kudi don gyaran hali; da gyara ta’adin da ‘yandaba suke yi, kamar kona dukiyar gwamnati; da kiwon lafiyar wadanda aka raunata; da asarar rayukan da aka halaka; da rasa aikin da ‘yandaba za su yi daa sun zamo sahihan mutane.

Kasa baki daya ta yi tata asarar: ga mummunan suna; ta yi fama da karurar hadura, da karuwar laifuffuka; ga gurgunta tattalin arziki (gwamnatin Scotland ta yi asarar £2.25b a shekarar 2005, dalilin shaye-shayen matasa). A campaign na wayar da kai kawai, gwamnatin England ta kashe £10m a wannan shekara ta 2005.

INA MAFITA?

Babbar mafita tana ga samar da sahihin shugabanci: wajibi ne shugabanni su gwada misali wajen sadaukar da kai, da bin doka da oda, da amana a rikon dukiyar al’umma, da adalci wajen jagoranci.

Wajibi ne a samar da wadatattun makarantu, da isassun malamai da kayan aiki; a bude hanyoyin samun aiki ga jama’a, kamar ta hanyar samar da wadatacciyar wutar lantarki, da isashen ruwan sha, da gyaran kasuwanni da tashoshin mota, da saukaka hanyar bude masana’antu da kamfanoni; a takaice dai wajibi ne a rage radadin talauci a cikin al’umma.

Daga cikin abin da ya bambanta matasan da da na yanzu shi ne goyon bayan da matasan da suka samu daga magabata: a gida matasan da sun samu tarbiyya, da kulawa da saiti; a waje ma suka samu hakan, kamar yadda ake bada labarin yadda Sardauna ya rika samawa matasa aiki ba sai ya san ‘ya’yan waye ba; akwai bukatar matasan yanzu ma su samu irin wannan gatan.

Su ma matasan na yanzu kuma sai sun taimaki kansu da kansu: su dage wajen neman ilimi, da neman halaliya; su kaucewa maula, da zaman kashe-wando; su san ciwon kansu; idan da za su lura fa dan abin da ake ba su suna yin daba bai taka kara ya karya ba; hasali ma su aka fi bai wa kudi kadan a harkar siyasa, idan da za a kwatantasu da jaim’an zabe, da jami’an tsaro, da kungiyoyi masu sa ido a harkar zabe, da sarakunan gargajiya, da wasu ‘yan jaridar, da wasu masu shari’ar zaben, da makamantansu, alhali aikin da ake sa matasa ya fi na kowa muni da ma wahala!

Ya kamata matasa su samarwa da kansu kungiyoyin kula da matasa da jin dadinsu; wannan zai sa su kansu su rika koyar harkar shugabanci, kamar bin hanyoyin fitar da shugabancin kungiya; su koyi campaign, da tsara zabe, da cike-ciken form, da biyan kudin kungiya, da biyayya ga shugabanci; sannan za su fi iya yakar munanan halaye a cikinsu da kansu.

Wajibi ne matasa su kyautata dabi’arsu ta zabe ta yadda za su rika zabar jam’iyyar da ta fi kyawawan tsare-tsare na kula da matasa; su tabbatar sun tashi tukuru wajen ganin sai jam’iyyar da suke so ne kadai ta kai labari a zabe; wannan zai wajabtawa wasu jam’iyyun rigeggeniya wajen fitar da tsarin inganta rayuwar matasa.

Jam’iyyun siyasa za su iya   rigeggeniya wajen tsari game da rayuwar matasa ta hanyar tsara yadda za a rika saka matasa a matsayin masu ruwa-da-tsaki game da duk wata harka da ta shafe su: misali, za a iya bai wa matasa gurbi a hukumomin kula da ililmi na matakai daban-daban; da wakilci a hukumar kula da wasanni; da hukumar kula da sana’o’i; da ta kula da harkar kasuwanci; da makamantansu; wannan zai bai wa manya damar sanin abin da matasa suka fi so, da yadda canjin zamani yake shafar su, da amfanuwa da tunaninsu wajen fid da tsare-tsare; ga kuma babbar magana ta bai wa dan’adam ‘yancin sa baki a abin da ya shafe shi wanda yake sawa ya ji zai iya komai don kare martabar wannan abin.

Haka kuma matasa za su iya tsoma baki a yadda ake tafi da mulkin kasa baki daya, musamman idan za su yi bincike na ilimi su tinkari masu ragamar mulki da sakamakon binciken: misali, me ya sa duk tsawon lokacin da aka dauka da samun mulkin kai a Nijeriya, wanda matasa ne jigon hakan, kamar yadda muka ambata tun farko, Nijeriya ta kasa samar da sahihin tsarin ci gaban matasa; aka fi kashe kudi a harkar tsaro a madadin samar da aikin yi? Me ya sa aka fi kashe kudi a samar da kotunan hukunta kananan yara a maimakon samar da dakunan karatu ko wuraren shakatarwar yara? Me ya sa aka fi samarwa ‘yansanda motocin sintiri a madadin samar da santocin koyar da sana’a? Me ya sa aka fi kashe kudi a gidajen kurkuku a kan samar da santocin gyara tarbiyyar masu shaye-shaye? Me ya sa aka gwammace biyan makudai wajen zuwa duba lafiyar shugabanni a kasashen waje a madadin gyaran asibitocinmu da inganta rayuwar ma’aikatan kiwon lafiyarmu? Me ya sa aka kasa canza wannan halin da aka gada daga ‘yanmulkin mallaka?

Akwai kuma bukatar gyara dokokin da suka shafi zabe, a rage maganar tara. A tanadi hukunci mai tsanani ga duk wanda aka samu da laifin bai wa matasa kayan maye ko kudin sayensu don su yi masa daba; misali, a hana mai irin wannan laifin shiga zabe, ko a soke zaben da ya ci, ko a kwace kujerar mulkinsa, ko a zartar masa da daurin rai da rai; da makamancin haka.

Idan matasa da manya suka yi iya kokarinsu wajen samar da canji nagari sai kowa kuma ya dukufa wajen addu’ar Allah ya inganta rayuwar matasanmu, su nesanta da harkar daba da ta’ammali da kayan maye. Allah Ta’ala ya yi alkawarin canza halin al’ummar da ta yi kokarin canza halin da take ciki maras kyau; canjin kuwa ya hada da imani da aiki nagari.

Allah Ta’ala ya agaza mana.

Wassalamu Alaikum.

SendShareTweetShare
Previous Post

Ko kun san?

Next Post

Ziyarar Gani da Ido: Wuraren Tarihi Masu Ban Mamaki a Jihar Katsina

RelatedPosts

APC

Canjin APC Ko Canjin Rigar Mahaukata?

by Sulaiman Ibrahim
3 days ago
0

Abubuwa sun bi sun damalmale, komai ya rincabe, kayan masarufi...

Shekarar

Shekara Kwana: Bankwana Da Shekarar 2020 (3)

by Muhammad
4 days ago
0

Wani mahimmin batu da ya kamata ace an yi bitarsa...

Shugaba Sam

Bankwanata Da Shugaba Sam

by Muhammad
5 days ago
0

Abdulrazaq Yahuza Jere, Da farko kafin in bayyana bankwanata da...

Next Post

Ziyarar Gani da Ido: Wuraren Tarihi Masu Ban Mamaki a Jihar Katsina

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version