Ya tsaya a gaban taro a wani dakin taro da ke Harlem na birnin New York. Ya fara jawabi ke nan ba a jima ba sai hayaniya ta barke daga bangaren mahalarta taron da sun kai mutum 400. Babu jimawa sai wani ya kutso zuwa gabansa a cikin wannan dakin taro, ya fitar da bindiga, ya harharbe shi da ita. Wasu mutum biyu ma suka zo suka kara daddanna masa dalma. An ce kimanin harbi 21 aka yi masa a wannan lokaci. Ya fadi magashiyan. Ya yi bankwana da duniya.
To kuma dama dai, kafin wannan rana da kimanin mako guda, wato a ranar 15 ga watan na Fabrairu, cikin dare, aka zo kofar gidansa da ke birnin na New York aka wurga wani abu mai kama da nakiya. Amma sai aka yi sa’a matarsa Betty Shabbaz da ‘ya’yansa hudu da ke cikin gidan suna barci ba su ji ko da rauni ba, sun tsira. Abin mamaki an kuma rasa wanda za a jingina wa laifin wannan ta’annati.
An ce a ranar da aka kashe shi, ya ki yarda masu tsaron kofar shiga dakin taron su yi aikin binciken masu shiga. Kazalika an ce ba a ga gilgilmawar jami’an tsaron birnin New York ba kamar yadda aka saba idan yana muzahara ko yana taro. Kuma an ga wani sakon telegram da aka aika ofishin FBI daga Daraktan hukumar, J. Edgar Hoober, tun kimanin shekara guda kafin wannan rana da aka kashe shi, inda aka rubuta cewa “Yakamata ku yi wani abu a kan mutumin nan.”
Dalilai makamantan wadannan da ke da rudarwa ga sanin hakikanin abin da ya faru suka sa wasu manyan masana da mufakkirai a Amurka suka ce dole a sake bitar bincike a kan yaya aka yi aka kashe shi, kuma waye hakikanin wanda ya sa a kashe shin. Haka mujallar Time ta wallafa.
Wane ne shi din?
Malcom d ne! Mutumin da aka kashe shi a 1965 saboda tsagwaron fadin gaskiya da son ganin al’ummar bakar fatar Amurka ta samu ‘yanci da zaman lafiya.
Ya faro rayuwarsa a matsayin dan Pastor. Aka kashe mahaifinsa saboda kare hakkin bakar fata a lokacin bai wuce shekara uku ba. An ce ‘yan Ku Klud Klan ne, kungiyar da ke ganin fifikon Bature sama da kowa tare da tsanar bakar fata. Mahaifiyarsa kuma aka kaita asibitin mahaukata. Hakan ya sa shi yawon gidaje da unguwanni da yankuna. Da ya kai shekarun samartaka sai ya zama dan iskan unguwa. Bai da aiki face shaye-shaye da ta’annati. Ya fasa wani gida don sata, aka kama shi, aka kai shi gidan yari na shekara 10. A can ne ya yi ta karanta litattafai. Kuma ya hadu da Elijah Muhammad shugaban kungiyar Nation of Islam.
Wannan haduwa ta natsar da shi kuma ta ba shi alkibla a rayuwa. Azama da hazaka da zalakar harshensa suka taimaka ya maida membobin Nation of Islam daga mutum 1,200 zuwa mutum 75,000 a cikin shekara 10. Ya zamo shi ne mutum na biyu mafi tasiri a wannan kungiya. Daga nan sai hassada ta kunno kai tsakaninsa da maigidansa Elijah Muhammad. Daga baya kuma ya samu maigidan nasa da laifukan masha’a da kananan yara, haka littafin Malcolm d: A Life of Reinbention ya ce. Elijah Muhammad ya kafa masa takunkumin rashin magana. Amma yanayin Malcom d na fadin gaskiya ya kasa hana shi magana a lokacin da aka kashe Shugaban Amurka John F. Kennedy. Ya yi wata mashahuriyar magana a kan kashe shi: “Abin da Amurka ta shuka shi ta girba.” (the chickens coming home to roost.) Daga nan kowa ya kama gabansa. Malcom d na ganin bai kamata a cutar da al’ummar bakar fata amma su ki ramawa ba. Shi kuma Elijah Muhammad na ganin duk abin da aka yi wa bakar fata na cutarwa to su kau da kai, su hakura. Wadannan fikirori biyu sun kara farraka
tsakaninsu. Malcom d ya je kafa tasa kungiyar, ya kuma samu nasa mabiyan. Ya je aikin hajji ya ga yadda fararen fata ke girmama shi duk da shi baki ne. Tunaninsa dungurungum ya canza game da kallon da yake wa ilahirin fararen fata. Ya dawo Amurka, ya kara tsara yadda zai samar wa bakar fata ‘yanci kuma ya cicciba mu su matsayi.
A wannan lokaci ya rika fuskantar barazanar kisa daga bangarori biyu: bangaren tsohuwar kungiyarsa Nation of Islam da bangaren FBI. Ya ce wa Aled Haley a littafin Autobiography of Malcom d As Told To Aled Haley, ya lura masu son kashe shi jami’an gwamnati ne. Don ya san dabarun ‘yan kungiyar Nation of Islam saboda shi ya koya mu su yawancin dabarun. Haka dai abin ya kai ga kashe shin a ranar irin wannan shekaru 55 da suka gabata.
Ba a yi karambani ba idan aka ce, al’ummar bakar fatar da ke Amurka ba ta taba samun mutum mai fikira da nagarta da son al’ummarsa tsakani da Allah irin Malcom d ba.
Marubucin Ossie Dabis ya ce: “Malcom d shi kadai yana wakiltar al’ummar bakar fata ce da ke raye.”
Zantukansa sun zamo tamkar gwala-gwalai ga masana kamar yadda rayuwarsa ta zamo. Domin suna zaburar da mutum ga sanin ‘yancin kansa. Ga misalan wasu ‘yan kalilan daga ciki:
“Ilimi shi ne fasfot din goben mutum. Domin gobe ta wanda ya shirya mata ne.”
“Ba za ka iya bambanta zaman lafiya da ‘yanci ba, domin babu mai zama lafiya face yana da ‘yanci.”
“Idan ba ka kula ba, jaridu za su sa ka tsani mutanen da ake zalunta kuma ka so wadanda ke zaluncin.”
“Ka zauna da kowa lafiya, ka zama nagari, ka bi doka, ka girmama kowa, amma in wani ya nuna ka da dan yatsa, aika shi barzahu.”
“Ina goyon bayan gaskiya, ko da kuwa wa ya fade ta; haka ina goyon bayan adalci, ko da kuwa a kan wa ya fada.”