Dakta Aliyu Ibrahim Kankara" />

Tunawa Da Majigin Baban Larai

Iya Mu’utasim Ibrahim dan Iya Labarana (1913-1952) wanda ya yi hakimcin Gundumar Bakori daga 1952 zuwa 1956 ya bayar da gagarumar gudunmuwa wajen ci gaban gari da gundumar Bakori gaba daya da har yau ake amfani da su. Kamar bayan ya zama hakimi a shekarar 1952, Iya Ibrahim ya zama mai kyakyawar dangantaka ga jama’arsa, mai kuma son zuwan baki a gundumar sa. Wannan ne ma ya sa ya bada izinin shirya wasan kwaikwayo na Hausa na Baban Larai a kasar sa watau a nan Bakori din. Wani abin sha’awa shi ne har ma ya zamo cikin masu wasan kwaikwayon a matsayin shugaba.

Yanda hidimar gabatar da majigin ta ke shi ne : Su Alhaji Iro Gawo Katsina (wanda ya halarci makarantar Middle ta Katsina, sannan aka tura shi Bauchi bangaren yada labaru na En’E. Shi ma Malam Baraya takwaran Gawo ne amma a En’E ta Katsina. To sai su ka yi canji Gawo ya koma Katsina, Baraya ya koma Bauchi. Amma da Gawo ya zo Katsina ya tarar Malam Yusuf dan marigayi Sarkin Katsina Abubakar shi  ke rike da wannan bangare na yada labaru. Da ya gusa gaba sai Gawo ya samu damar zama babba mai kula da wurin) su suka yi yawo su ka ragade Arewacin Kasar nan  suna nune-nunen majini. Sun sha rana kamar bisan daki, sun sha raba kamar karen daji wajen yayata manufofin gwamnati a kan aikin gona a arewacin Najeriya. Sun taimaka kwarai da ainun wajen fadada wannan sha’ani.

Asalin wannan majigi shi ne sashen watsa labaru na gwamnatin arewacin Najeriya, bangaren fim ko majigi (Northern Nigerian Information Serbice) su ka ga ya dace su shirya wannan abu na yayata shirin gwamnati na aikin gona.  Babu shakka saboda tallar gyada da auduga aka yi ta wannan hayagaga ta tallata abin. An kuma yi nune-nunen shirin  a tsakanin farkon 1950 zuwa 1976 har ma da farkon shekarun 1980. A wannan wakati wakar da ta fi tashe don tallata wa talakawa shirin ita ce ta Hakananne Mamman kanen Idi Wan Yalwa ta Baban Larai wadda marigayi Dokta Mamman Shata Katsina ya yi.

‘…..ya yi gyada ya yi auduga Baban Larai/

Baban Larai shi ne Alhaji Abdullahi Abubakar Song, shi ne darakta a wannan ma’aikata ta yada labaru, don haka ne ma ya zama shi ne tauraron shirin, wanda daga baya ya taba yin sakataren dindindin na tsohuwar gwamnatin jihar Gongola cikin 1976 din. Ita kuma matar sa a shirin ana ce da ita ‘burodi’ mutumniyar Bakori ta jihar Katsina ce, kuma ita ba ma’aikaciyar gwamnati ba ce, a nan Bakori su ka same ta. Shi dama Shata dan gida ne a Bakori don ya zauna garin daga watan Yuni na shekarar 1943 zuwa 1954, sa’annan ya tashi ya koma Kano da zama. Shata ya dade Bakori, har ma wasu da dama su na zaton shi haifaffen nan ne.

Ban da sha’anin amfanin gona kuma majigin ya yi aikin ragade arewacin kasar nan wajen nuna sauran sana’o’in Hausa kamar su dambe da kokowa da sharo da sauransu. Duk gari sai a ware watarana da dare a kawo motar da ke nuna majigin a kofar gidan Sarki ko Hakimi. A tara jama’a a nuna masu. Wani lokaci kuma akan nuna shi a fili, bal allai azimun sai kofar gidan maigari ba.

To ba ma ta hanyar majigin Baban Larai kawai aka yayata shirye-shirye da manufofin gwamnati ba a Arewacin Najeriya, bil hasali ma tun daga 1958 da aka fara bude tashar rediyo a Arewa aka fara yin kahan. Musamman ma gidan rediyon BCNN Kaduna. Ana zaton wannan majigi da aka yi amfani das hi aka yayata Shata shi ya haifi zuwan Shata BCNN na Kaduna da kuma karamin gidan Rediyon Sarauniya na Tudun wada Zariya. Hakika a nan ma   Shata ya sami dammar yayata Arewa da arzikin da ta mallaka. Bayan baiwa Najeriya ‘yanci akwai gidajen rediyo da aka bude mallakar jihohin arewa: kamar an bude  a Sakkwato da Ilorin da Jos da Maiduguri da Kano da Enugu da Ibadan, masu amfani da 49 meter Band watau gajeren zango, ma’na ana iya jinsu a wuri mai nisa. A shekarar 1977 (bayan Janar Murtala Ramat Mohammed ya kirkiro jihohi cikin 1976) sai aka kirkiro wasu gidajen rediyon suma mallakar jihohi a garuruwan Minna, Makurdi, Akure, Abeakuta da Owerri,su kuma suna amfani da matsakaicin zango watau ba su da nisan zango ke nan, watau inda rediyon zai iya kaiwa ba wani wuri mai nisa ba ne. Wadannan gidajen rediyo sun taimaka gaya wajen yayata Mamman Shata Katsina. Galibi suna amso wakokin sa daga karamin gidan rediyon Zariya da rediyon jihar Kaduna(a yanzu) da kuma babban gidan  watau RTK ko rediyon Tarayya Kaduna da ake magana a kansa.

Domin kirkiro wasu shirye-shirye da za su ci gaba da kayatar da jama’a gidan Telbijin na RTK din ya kirkiro da shirin Gidan Kashe Ahu, inda aka rika yin wasanni na barkwanci tare da kiran mawaka su yi wasa. A nan ana yin dabarun nuna wa mutanen mu na Arewa muhimmancin aikin gona, watau irin dai abubuwan da Sardauna ya so mutanen Arewa su mayar da hankali a kai. Shugaba Inunu mai dankalin Turawa na Kaduna shine ya zama Alhaji a kalkashin shirin, tunda shine kusan mai iko a ‘yan kulob na Zabi Sonka. Sai kuma Hajiya Hajara Ibrahim ma’aikaciyar gidan da ta zama matarsa ko Hajiya a shirin. To tun cikin 1979, a cewar Sani Gwarzo Tumbuleke ake kiran Shata akai-akai ya na yin wakoki. Shi Sani Gwarzo shine ya zama kamar dansu, wanda ya ke raggo ba ya son yin noma sai dai ya ci abinci kurum. Gwarzo ya ce a Funtuwa aka fara yin shirin kashe Ahu din, a cikin 1976 a Mairuwa Motel. Aka yi shela a ranar, kuma kusan duk Funtuwa ta taru can. To a nan Shata ya fara yi masa waka. Daga nan Gwarzo ya zamana a tsakanin RTK da Mamman Shata; duk sa’adda za a yi was an shi ake turawa ya nemo makadin. To sabili da Shatan ya lura Tumbuleke ya na da rikon amana da kuma hankali sai ma ya rika jan shi sun a yawo tare a wasu lokuta. Sun zagaya garuruwa kamar su Lafai, Nasarawa (ta Lafiyar Bare-bari), Kwantagora, Minna, da sauransu. Da an duba bangaren Jaddawali za a ga jerin wakokin da Shatan ya yi ma mahukuntan gidan Kashe Ahu din barjat. Gwarzo ya ce shigar Shata Gidan Kashe Ahu ya habaka gidan ya kuma kara masa farin jini. Amma a shekarar 1984 aka daina yin shirin.

Mu kwana nan. 

Exit mobile version