Bishir Dauda" />

Tunawa Da Marigayi Janar Shehu Musa Yar’aduwa

Hausawa na cewa, ba rabo da gwani ba, maida gwani. Marigayi Manjo-Janar Shehu Musa Yar’aduwa (Allah ya jikan shi; ya yafe masa,ya rasu ranar 8 ga Disamba,1997), na daya daga cikin manyan ‘yan kasarmu da tarihi ba zai taba mantawa da shi ba. Musamman yanzu da wasu halaye na dattako da sadaukarwa sukai karanci tsakanin matasan ‘yan siyasa masu tasowa.
Shin me za mu koya daga rayuwa da gwagwarmayar wannan jarumi? Jarumtarsa, a matsayinsa na soja, wanda ya samu damar halartar makarantar horon soja ta alfarma dake Ingila wato Sandhurst?, kuma da jarumtarsa da ya nuna a lokacin yakin basasar Najeriya? Koko za mui maida hankali kacokan mu dubi tarihin siyasarshi, da irin gudunmuwar da ya bada a siyasance a Najeriya? Koko bangaren harkokin kasuwancinsa da nasarorin da ya samu a harkar kafa masana’antu za mu duba? Koko za mu duba rawar da ya taka wajen yaki da kabilanci ko bangaranci? Ko juriya da jajircewa da ya nuna da ta kai shi rasa ransa a gidan wakafi? Kota ina mutum ya duba, zai ga lalle wurin nan an yi jarumi, kuma nagartaccen mutum wanda ya daga sunan jiharsa, zuri’arsa dama Najeriya bakidaya.
Shakka babu, Shehu Musa Yar’aduwa, ya tashi daga gidan Sarautan kuma gidan mulki, domin mahaifinshi, marigayi Musa Yar’aduwa, baya ga sarautar, kuma ya yi minister a lokacin janhoriya ta farko, a matsayin ministan Birnin tarayyar Najeriya na wancan zamani wato Legas. To amma duk da kasancewa, Shehu ya tashi cikin gata da wadata, za mu fahimci, yadda ya bambanta da takwarorinsa, wadanda suka tashi cikin gata da wadatar. Misali, akwai ‘ya’ya da yawa da suka tashi cikin daula, suka samu dama, amma damar da daular bata amfane su ba. Hasalima, sai suka rungumi miyagun dabi’u kamar shan giya da shaye-shaye, sace-sace, zinace-zinace, daga karshe basu tsinana komi ba, kuma basu dabbaka tarihin gidajen nasu ba. Raggo, mashayi, dolo, lalatacce bai iya soja, ko ya yi, to ba zai tasiri ba, domin aikin soja, aiki ne na tarbiya da jarumta. Wannan kawai ya isa, ya nuna maka, kowaye Shehu Musa Yar’aduwa. A soja ma, shi ba kurar baya bane. Domin ko a wancan lokaci dake akwai dama da yawa, to ba kowane sakarai bane ake dauka a kai Sandhurst. Duk matsayinka da gidan da ka fito.
Kashe Janar Murtala Ramat Mohammed, an samu sauyin gwamnati, inda Obasanjo ya zama shugaban kasa na mulkin soja, yayin da Shehu Musa Yar’aduwa ya zama mataimakinshi. Tarihi ya nuna gwamnatin mulkin Obasanjo da Shehu Musa Yar’aduwa, ta nuna gaskiya wajen aiwatar da dukkanin tsare-tsaren da gwamnatin Murtala ta bari, muhimmi shi ne, mayar da Najeriya bisa Dimokaradiyya. Basu bar gwamnati ba, saida suka tabbatar an rubuta sabon kundin tsarin mulki, sannan suka shirya tsabtataccen zabe, suka mika gwamnati ga farar hula a 1 ga Oktoba, 1979. Kada mu manta gwamnatin Murtala/Obasanjo gwamnati ce da ta ceto kasar daga mulkin Yakubu Gowon, da bayan kamala yakin basasa ya kasa mayar da mulki ga farar hula. Mun san irin ci gaban da aka samu a lokacin Murtala/Obasanjo.
Fagen siyasa, za mu ga Shehu Musa Yar’aduwa, tun Sardauna, ba a kara kasurgumin dansiyasa a Arewa kamar shi ba. A Arewa ba a samu dan siyasa da ya samu karbuwa daga dukkan sassan kasar nan-Yarbawa,Ibo,kudu maso kudu, tsakiyar Najeriya, ko’ina yana da yara,barori da abokan siyasa, masu bin bayan shi.Ga sunan su Solomon Lar,Anthony Aneni,Atiku Abubakar,Muhammadu Kwairanga Jada,Babagana Kingbe da sauran su. Wannan yasa ake mai kirari a fagen siyasar Najeriya a matsayin gada mai hada zumunci (Bridge builder). Za mu ga tasirin siyasar Shehu Musa Yar’aduwa a lokacin tsarin maida Najeriya mulkin Dimokaradiyya na Janar Ibrahim Badamasi Babangida, inda , Shehu ya kafa jam’iyyun PF da PDM, ya kuma assasa jam’iyyar SDP, duk da haramta mashi shiga siyasa da waccan gwamnati tai, sannan ya taka rawa wajen ganin MKO Abiola ya ci zabe a wancan lokaci.Wasu na kamanta siyasar Shehu Musa Yar’aduwa da irin ta Awolowo, ni a fahimtata, siyasar Shehu Musa Yar’aduwa ta bambanta, tunda shi ne, ya fara yakar siyasar kabilanci ko shiyya a Najeriya. Awolowo jam’iyyarsa ta AG, asalinta kungiyar kabilar yarbawa ce wadda ake kira da Ogbe-Omo-Odudua. Kuma Awolowon nan, ya yi amfani da kabilanci a siyasar janhoriya ta farko, hatta a jam’iyyar matasan Najeriya (NYM) lokacin mulkin mallaka. Shiko Yar’aduwa ma,wasu na ganin ma ya fi fifita wani yankin da yankinsa.
Abin tambaya shi ne, yanzu yadda ake siyasar banza ta rashin alkibla, siyasar neman abinci da neman kudi, ko mi Yar’aduwa zai ce idan da ace zai dawo Duniya? Dubi fa, yadda ‘yan siyasar yanzu suka raina mutane, yau suna waccan jam’iyya, gobe suna wata. Abin mamaki hatta ‘tsaffin ‘yan siyasa irin su Rabi’u Musa Kwankwaso wanda ya yi siyasa da Shehu Musa Yar’aduwa, amma suke wata irin siyasa? Dubi Sule Lamido, wanda kema kanshi kirari da Janar na siyasa, amma yake bari, ‘yandagaji na latsa shi, saboda ya saki layin siyasar Yar’aduwa.
Inda Shehu Musa Yar’aduwa, irin wannan banzar siyasar yai, to da lokacin da Babangida ya haramta masu shiga siyasa, sai ya zama munafuki, ma’ana, ya zama abin da a turancin siyasa ake kira da “sycophant”, ya tai ya bi Babangida yana lallabarsa da a tai da shi.Amma maimakon haka, sai ya zabi da ya mara ma, Abiola baya, su yaki gwamnatin sojar.
Da Shehu Musa Yar’aduwa na siyasar banza irin wadda ake yanzu, da bai mutu gidan yari ba. Da sai ya mika kai bori ya hau, ya bi Abacha, su sha dadi. Amma sai ya zabi ya tsaya bisa akidarsa. Shi yasa yake cewa “garkameni da Janar Abacha yai, na daya daga cikin sadaukarwa da za mui, domin ‘yantar da kasar mu” (My incarceration and ordeal in the hands of General Abatcha is a sacrifice some of us must make for our country to be free.)
Marigayi Umaru Musa Yar’aduwa, kane ga Shehu Musa Yar’aduwa, na daya daga cikin shugabannin Najeriya da tarihi ba zai taba mantawa das u, a wurinshi mun ga horo na Shehu. Ko mutum ya ki, ko ya so, Atiku Abubakar Wazirin Adamawa, wanda daya ne daga cikin yaran Shehu Musa Yar’aduwa a siyasa na daya daga manya kuma kwararrun ‘yan siyasa a Afirika dama Duniya, nan ma mun ga tasirin Shehu. In dai mutum horon siyasar Shehu ne, kuma cikakken dan PDM ne, to za ka same shi, duk lalacewar shi, ya fi, ‘yan bankaura dake ta tsalle-tsalle yanzu a fagen siyasar Najeriya.
Babu abin za mu ce yanzu sai dai Allah ya jikan Shehu Musa Yar’aduwa, yasa kwanciya hutu ce.

Exit mobile version