Sharfaddeen Sidi Umar" />

Tunawa Da Shekaru 45 Da Kisan Gillar Janar Murtala Muhammad

Murtala Muhammad

Al’ummar Nijeriya a kowace shekara a ranar 13 ga watan Fabrairu suna tunawa da kisan gillar da sojoji suka yi wa Shugaban Kasa Janar Murtala Ramat Muhammad a lokacin da yake jan zaren mulki a yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a 1976.

A jiya gawurtaccen shugaban maras tsoro da fargaba ya cika shekaru 45 da bakuntar lahira a kisan da sojoji suka yi masa a bakar bahaguwar ranar da al’ummar Nijeriya ba za su taba mantawa da ita ba.

A ranar sojoji karkashin jagorancin Dimka sun budawa motar Janar Murtala wuta ne ba kakkautawa a lokacin da yake kan hanyar zuwa Masallacin Juma’a ta yadda ba tare da bata lokaci ba ya karbi kiran mahalliccinsa tare da ‘yan tawagarsa ciki har da dogarinsa Laftanar Akintunde Akinsehinwa da direbansa.

Janar Murtala Ramat ya karbi ragamar jagorancin kasa ne a yayin da sojoji suka nuna rashin gamsuwa tare da kosawa da mulkin Janar Yakubu Gowon wanda a kan hakan suka hambarar da Gwamnatinsa tare da dora shi a matsayin Shugaban Kasa domin kawo gyara kan barnar da sojoji da ‘yan siyasa suka yi.

A yau Nijeriya da al’ummarta na tunawa da mulkin Janar Murtala a matsayin jajirtaccen hazikin gwarzon soja wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen bautawa kasarsa da dukkanin karfinsa a kokarin sauke nauyin da ke kan sa a mulkin da ya hau a ranar 30 ga Yuli 1975.

Haka ma a na tunawa da hobbasar kwazon Janar Murtala Ramat Muhammad wajen  gudanar da shugabanci nagari, hada kan kasa da  kirkiro da sababbin Jihohi 7 tare da bayyana bukatar da ke akwai ta mayar da Birnin Tarayya daga Lagas zuwa Abuja da mayar da mulki ga Gwamnatin farar hula bukatocin da suka cika bayan kisan gillar da aka yi masa.

Jihohin da Murtala Ramat Muhammad ya kirkira a ranar 3 ga Fabrairu 1976, kafin kisan gillar da aka yi masa sune Bauchi, Benue, Borno, Imo, Niger, Ogun da Ondo bayan sun cika dukkanin sharuddan zama Jihohi wanda hakan ya kai Nijeriya ga samun Jihohi 19.

Tarihi ya adana zuwan Janar Murtala Ramat Muhammad a duniya a ranar 8 ga watan Fabrairu 1988 a Kano. Ya shiga soja a 1958. Bayan karatu a Kwalejin Barewa da ke Zariya, ya shiga aikin soja a shekarar 1959 a inda ya yi karatu a makarantar soji ta Royal Military Academy, Sandhurst da ke Burtaniya.

Bayan samun mukamin Laftanar a 1961, ya kara samun karin girman zama Manjo a shekarar 1964 tare da kula da sashin sadarwa a Hedikwatar Rundunar Soji da ke Kaduna.

Murtala Ramat wanda Janar Aguiyi- Ironsi ya yi wa karin girma zuwa Laftanar Kanal a 1966, ya taka muhimmiyar rawar gani a yakin basasar da aka yi a shekarar 1967 a lokacin da Laftanal Kanal Ojukwu ya yi kokarin balle yankin Kudu -Maso-Gabas daga Nijeriya a kokarin kafa yankin Biafra.

Murtala Ramat ya nuna jarumtaka da kwarewa da gogewa wajen jagorantar Rundunar Sojojin da suka murkushe mayakan Biafra ta hanyar kawo karshen yakin bakidaya a 1967.

Murtala Ramat yana da mukamin Birgediya Janar a lokacin da sojojin da suka yi juyin mulki na uku a Nijeriya suka nada shi a matsayin Shugaban Kasa. A watan Janairu 1976 ya samu karin girma zuwa Janar wato soja mai anini hudu bayan ya rike Birgediya da mafi kankantar shekaru 33.

Daga cikin abubuwan da ake tunawa da Tsohon Shugaban akwai filin jirgin saman kasa da kasa na Murtala Muhammad da ke Lagos da babban filin taro na Murtala da Asibitin Murtala da daidaikun wurare. Haka ma a shekaru biyu bayan rasuwarsa a ranar 13 ga Fabrairu ta kasance ranar hutu.

Janar Murtala Ramat ya rasu ya bar mata daya, Ajoke Muhammad da ‘ya’ya shida wato A’isha, Zakari (ya rasu) Fatima, Abba (Riskua) Zaliha da Jummai. Abba ya kasance Mashawarci na Musamman ga Shugaba Obasanjo kan Sayar da Kadarori.

Exit mobile version