An kirkiro da ranar tuna wa da sojoji yan mazan jiya, wadanda su ka sadaukar da rayuwar su a fagen fama, a kokarin kare martaba da diyaucin kasar su, wanda ke zuwa 15 ga watan Junairun kowace shekara. An ware wannan muhimmiyar rana ce domin karrama su, wanda mu ke gani a kowace shekara a Nijeriya, sai dai abin tambaya: yaushe girmamawar zai tashi daga biki zuwa aiki?
Rana ce da aka ware domin karamma yan mazan jiya wadanda suka samu damar halartar Yakin Duniya na I da II hadi da na yakin Basasan Nijeriya. Wanda a farko an fara gudanar dashi 11 ga watan Nuwamban kowace shekara a matsayin girmama wa ga yan mazan jiyan da su ka halarci Yakin Duniya na daya.
Wanda bayan samun nasarar da sojojin Nijeriya su ka yi a lokacin yakin Biafra, ranar 15 ga watan Junairun 1970, ya jawo canja kalandar kasashen renon Ingila domin tuna wa da kawo karshin yakin Basan da Nijeriya ta sha fama dashi- shi ne ya koma 15 ga watan Junairun kowace shekara a matsayin ranar tuna wa da yan mazan jiya.
Bugu da kari kuma, wadannan yan mazan jiyan sun cancanci karrama wa ta la’akari da yadda suka sadaukar da rayuwakan su wajen kare martabar kasar su- alhalin suma suna son su rayu a wannan duniya tare da iyalai da yan uwansu, amma su ka hakura don kasa ta zauna cikin aminci da diyauci. Sannan wannan rana ce wadda ya dace a fadadata tare da sanya tasirinta a zukatan yan kasa baki daya domin ci gaba da martaba yan mazan jiya, ba wai sai a gun manyan jami’an gwamnati ba.
Har wala yau, a yanayi irin wannan, wanda Nijeriya ke fama da matsalolin tabarbarewar tsaro, akwai bukatar masu ruwa da tsaki a sha’anin gudanar da kasar nan su motsa tare da aikin karfafa gwiwar jami’an tsaro- musamman a irin wadannan ranakun tuna wa da yan mazan jiya, ta hanyar yi musu goma-ta arziki, wanda zai kara musu kwarin gwiwar aikin da suke na yaki da matsalar tsaro, wanda akasin hakan zai rage mu su karsashi a kokarin da suke yi.
A lokuta da dama an sha jin korafe-korafe daga bakin wasu daga cikin yan mazan jiyan dangane da yadda gwamnati ta yi watsi da lamurransu ballanta kuma wadanda su ka rasu. Wanda hakan zai jawo koma baya tare da dakushe karsashin jami’an tsaron da ke kan aiki. Saboda da na gaba ake gane zurfin ruwa. Lokaci ya yi wanda gwamnati za ta nuna karramawa ga yan mazan jiya a aikace ba taro ko biki ba kawai.
A hannu guda, zai iya kasancewa zolaya ace ana girmamaka amma hatta kudinka sallama bayan ritaya ace sun gagara. Wanda idan zamu tuna, ko a 2018 sai da tsuffin sojojin da su ka yi ritaya a Nijeriya su ka roki shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cika alkawarin da ya dauka a lokacin yakin neman zaben 2015 wajen rage musu radadin matsalokin da su ke fuskanta.
A wata tattaunawar da jaridar Guadian ta 5 ga watan Nuwamban 2018, jami’in hulda da jama’a na kungiyar tsuffin sojojin Nijeriya ta RANAO, Capt. Yusuf
Abdul-Malik ya bayyana cewa (a lokacin) har yanzu an kasa buyansu hakkokinsu, wadanda suka dace gwamnati ta basu ciki kuwa harda sabon kari.
Ko a wannan shekara ta 2020 sai da hukumar kula da fanshon tsuffin sojoji ta Nijeriya (MPB) ta koka wa majalisar dattawa tare da neman cewa ta dada kasafin kudin da take ware mata, saboda ta iya biyan tsuffin sojojin da su ka yi ritaya.
Shugaban hukumar MPB, Saburi Lawal, shi ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da kasafin 2021 wanda aka ware wa hukumar a gaban yan majalisar a kwanan baya, tare da nanata cewa kudin da ake ware wa tsuffin sojojin ya yi kadan.
“Sannan kuma kawowa yanzu, daga cikin wadancan kudin da aka ware wa hukumar, naira 163,195,174, 488 ne kacal aka fitar, wanda ya yi daidai da kaso 75 cikin dari na kasafin.”
Bisa wannan tare da dimbin matsalolin da tsuffin sojojin ke fuskanta- baya ga na yan mazan jiyan, ya dace gwamnati ta sake lale tare da zakudawa daga biki kawai zuwa ga aiwatar da shi a kasa ta hanyar bayar da cikakkar kula ga jami’an tsaron da su ka bauta wa kasa, su ka sadaukar da rayukan su don samun tsaron kasa da yan kasa.
Farko, a karrama wadanda su ka sadaukar da rayukan su wajen kare diyaucin kasa; na dauri da na yanzu- wadanda aikinsu ya nuna hakikanin yan kishin kasa ne, wanda ya dace ayi musu girmama ta musamman ta hanyar wanzar da sunan su don ci gaba da tuna wa da gudumawar da su ka bayar.
Abu na biyu, a nuna wa iyalai da yayan da su ka bari soyayya da kauna dangane da sadaukarwar dan uwa/mahaifi ya yi a lokacin da ake gudanar da irin wadannan bukukuwan, hakan zai sanya farinciki ga yan uwa da iyalan marigayan tare da yan mazan jiyan da suke raye kana sauran yan kasa su yi alfahari tare da girmama su a duk inda suka shiga, ko iyalansu. Idan mun lura, hakan wasu manyan kasashe ke yi wa hazikan sojojin da su ka yi kokari ko suka sadaukar da rayukan su wajen kare kasa don karfafa gwiwar wasu jami’an tsaro.