Khalid Idris Doya" />

Turai Yar’adua: Matar Tsohon Shugaban Kasa Da Ta Taka Rawa A Gwamnatin Mijinta

Ko-kun-san…

 

Hajiya Turai Umaru Yar’adua matar marigayi tsohon shugaban Nijeriya, Umaru Musa Yar’adua kuma tsohon gwamnan jihar Katsina, ta zama alkyabbar matan Nijeriya kasancewarta uwargidan shugaban kasa (First Lady) tun daga shekarar 2007 har zuwa rasuwar mijinta, Shugaban kasa Yar’adua a ranar 5 ga watan Mayun shekarar 2010?

Turai ta samu damar shiga a dama da ita a bangaren gudanar da mulkin Nijeriya sa’ilin da mijinta ke kan karagar mulkar kasar nan, ta bayar da gudunmawa ta fuskoki daban-daban wurin kyautata rayuwar mata da yara, a bisa haka ne filinmu ya taho da tarihin rayuwarta.

 

Wace Ce Hajiya Turai Umar Musa Yar’Adua?

 

An haifi Hajiya Turai Umar Musa Yar’Adua ce a ranar 26 July 1957 a jihar Katsina da ke arewacin Nijeriya. Ta halarci makarantar Firamare ta Garama da kuma sakandarin gwamati da ke Kankiya dukka a jihar Katsina a lokacin da take gabar yarantar ta. Daga bisani ta zo ta shiga kwalejin Katsina College of Arts, Science and Technology da ke Zariya a jihar Kaduna, hazakarya ya kaita ga samun nasarar lashe jarumar daliba da ta yi zarra a shekarar 1980 na wannan makarantar. A kuma shekarar alifi da 1983, Yar’adua ta amshi shaidar karatun digiri na farko a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya inda ta karanci harshen nasara (Ingilishi).

Hajiya Turai ta auri marigayi Umaru Musa Yar’adua a shekarar 1975, Allah ya albarkacesu da samun ‘ya’ya bakwai, maza biyu mata biyar; mazan sune Shehu Umaru Musa Yar’adua and Musa Umar Musa Yar’adua, daya daga cikin ‘ya’yansu mata ita ce  Zainab wacce ta auri Usman Sa’idu Nasamu Dakingari, tsohon gwamnan jihar Kebbi.

Daga cikin ‘ya’yansu da marigayi Umaru sun hada da; Aisha, Ibrahi, Zainab, da Nafisat Yar’adua matar tsohon gwamnan jihar Bauchi, Malam Isa Yuguda, Maryam ‘Yar’adu.

Ita dai Hajiya Turai Yar’adua ita ce mai dakin marigayi tsohon Shugaban Nijeriya na 13 Umaru Musa Yar’adua wanda ya mulki kasar daga 2007 zuwa 2010.

Ta kasance mai karfin fada a-kuma-ji a mulkin mijinta saboda yadda ta kasance daya daga cikin mashawarta ga Yar’adua a lokacin da yake mulki.

Wasu rahotanni sun nuna yadda Turai ta rika yin tasiri wajen zaben wasu daga cikin jami’an gwamnati da za su ba da gudummawa a gwamnatin mijinta

Ta kuma kasance gaba-gaba a jinyar mijinta marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’adua wanda ya yi doguwar jinya a kasar waje gabanin rasuwarsa.

Har ma wasu rahotanni na cewa sai wanda ta so yake ganinsa cikin manyan mukarrabansa da ke zuwa duba shi sakamakon karfin fadinta a-ji a karkashin gwamnatin marigayi Musa Yar’adua.

Hajiya Turai tana daga cikin matan da suke kokarin ganin rayuwar mata da yara ya ingantu, inda aka shaideta da bayar da gudunmawa wa marayu da matasa karfi, ko lokacin da take matar shugaban kasa ta yi ta fitar da shirye-shirye da tsare-tsare daban-daban domin karfafan mata da matasa ta fuskokin rayuwa daban-daban.

A gefe guda kuma, Turai tana da zimmar ganin an kawo karshen matsalar cin zarafin mata da ta’anmuli da miyagun kwayoyi a tsakanin jama’a, wanda a yanzu haka ma ta sake tashi tsaye domin ganin an kai ga samun natija wurin shawo kan matsalolin.

 

Exit mobile version