Turke Yara Gazawar Gwamnati Da Malamai Ce – Sheikh Khalil

Shugaban Majalisar Malamai ta kasa reshen Jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, ya bayyana cewa, kowa ya na da hannu bisa rahotani da ke nuna yadda iyaye ko marika yara ke turke yara da hukumomi su ke ganowa a ceto su daga kangin azabtarwa da su abu ne mai kyau, ya na mai cewa, akwai gazawar gwamnati da malamai, ba iyayen yaran kadai ba.

Sannan abin da iyaye musamman wani da ake jin aikin kishiyar uwa ne da suke daure yara a wasu gidaje, wannan duk gurbacewar tunanin alumma ne, kuma guguwar bala'i ce ta samu alumma sai dai fatan kawar da wanan alamari ta hanyar aiki da neman taimakon Ubangiji.
Shehun Malamin ya bayana haka ne a cikin shirinsa na Fahimta Fuska ne da ya ke gabatarwa a Gidan Redion Kano duk ranar Juma’a a kowa ne mako, ya ce dole ne sai gwamnati a kowa ne mataki ta yi aiki tukuru wanda ya kamace ta ta samar da mafita ga al’uma kamar da gwamnati ta rushe Gidajen mari bata samar da madadinsa ba, an dai rushe kawai ba manufa kenan ta rushewa, wanda bai kamata ya zama haka ba, dole idan hukuma ta samu jama
a na wani abu da take ganin akwai kuskure ta kawo nata inta hana mai kuskuren da ta gani.
Haka su ma Malamai su yi aiki tukuru a Masallatai da wurin karatutukansu na yau da kullum na gyara tunanin mutane ta hanyar fadakarwa da jan hankali da ilimi domin ilimi ba hankali babbar matsala ce ya zama wajibi a kawar da gurbataccen tunani a tsakanin alumma.
A karshe ya ce akwai bukatar su ma kafofin yada labarai su hada kai wajen fito da shirye-shirye mai kama da juna wanda zai dai dai ta tunanin jama
a ba gurbata shi ba, kuma a dade ana yi ba a yi wata uku a bari ba ai tayin sa kamar yadda ya kamata wannan shi ne aiki da kowa zai yi domin gyaran wanan al`uma don fita daga wannan Guguwar bala’i.

Exit mobile version