Rabiu Ali Indabawa" />

Turkiyya: Trump Ya Aika Da Sako Mai Harshen Damo

Shugaban Amurka Donald Trump ya aikawa da Turkiyya wasu sakonni biyu masu karo da juna dangane da shirin da kasar ta Turkiyya ke yi na kai farmaki kan mayakan Kurdawa.
A jiya Litinin Shugaba Trump ya ce, dakarun Amurka za su ja gefe domin shirin kai farmakin da Turkiyyar ke yi, sai dai ya gargade ta cikin kakkausan harshe da cewa, idan har ta wuce makadi-da-rawa wajen kai hare-haren, zai dauki matakan kassara tattalin arzikinta.
Sai dai abokanan shugaban Amurka ‘yan jam’iyyar Republican, sun nuna fushinsu kan yadda Amurkan za ta yasar da Kurdawan Siriya, wadanda suka hada kai suka yaki mayakan IS tare da sojojin Amurka.
A jiya Litinin, daya daga cikin magoya bayan Trump a majalisar dattijai, ya kira wannan mataki a matsayin “rashin hangen nesa da sanin ya kamata.”
Hakazalika, ‘yan jam’iyyar Democrat, ma’aikatar harkokin waje da ta tsaron Amurka, duk sun nuna kin amincewarsu ga wannan mataki na shirin kai hari da Turkiyyan take so ta yi a arewacin Syria.

Exit mobile version