Connect with us

LABARAI

Turnuku A Jihar Osun: PDP Ta Shammaci APC

Published

on

…Hukumar INEC Ta Ce Zaben Bai Kammala Ba

Ya zuwa yanzu ana iya cewa, Jam’iyyar adawa ta PDP ta shamaci jam’iyyar APC a zaben gwamnan jihar Osun wanda bai kammala ba.

Lissafin Hukumar INEC a zaben gwamnan Jihar Osun wanda aka fara fafatawa shekaran jiya zuwa jiya ya tabbatar da cewa kuri’u 3,498 suka hana a ayyana nasarar jam’iyyar adawa ta PDP.

Hukumar Zabe ta Kasa, INEC ta bayyana cewa zaben Gwamna na Jihar ta Osun bai kamala ba a jiya, bayan da aka samu kuri’un da ba a iya tantance su ba. Inda kuma hukumar ta INEC ta ayyana ranar 27 ga wannan watan na Satumba domin kammala zaben a wasu rumfuna.

Bayan kammala kirga kuri’un da suka shigo hannu, Dan takarar Jam’iyyar PDP, Nuruddeen Adeleke ne ke gaban ‘yan takara 48 da suka shiga sahun neman kujerar ta gwamna.

Hukumar ta INEC ta ki ta ayyana Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben ne saboda tazarar da ya ba takwaransa na APC ba wani abin a zo a gani bane, kuma komi na iya faruwa idan aka kammala gyaran kuri’u 3,4Hukumar ta INEC ta ki ta ayyana Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben ne saboda tazarar da ya ba takwaransa na APC ba wani abin a zo a gani bane, kuma komi na iya faruwa idan aka kammala gyaran kuri’u 3,498 da suka rage yayin da yake bayyana sakamakon zaben, Shugaba mai sa ido akan zaben, Joseph fuope , wanda shi ne Shugaban Jami’ar Kimiyya dake Akure, ya ce, a halin da sakamakon yake ba zai iya ayyana Adeleke a matsayin wanda ya lashe ba, kamar yadda dokar hukumar ta tanada.

Adadin kuri’un da aka sauke a rumfuna bakwai sun kai 3,498, wanda ya zarce yawan kuri’un da PDP ta wuce APC da su.

A garin Osogbo, lamarin ya shafi rumfar zabe daya, rumfar zaben nada masu jefa kuri’a 884, jami’in lura da zaben ya bayyana cewa, babban jami’i mai kula da zabe a yankin gaba daya ne ya karbi takardar dake dauke da bayanan sakamakon zaben gaba daya ba tare da wani bayani ba.

A tattaunawar da ya yi da manema labarai, Kamishinan zabe mai kula da wayar da kan masu jefa kuri’a da watsa labarai, Mista Solomon Soyebi, ya ce, bambancin dake tsakanin jam’iyyu biyu dake kan gaba a jerin sakamakon daben ya nuna kuri’u 353 kawai ne.

“Yawan masu jefa kuri’a a rumfar daben da aka soke ya kai 3, 498. Saboda haka a matsayina na jami’in zabe, ba zai yiwu ba in ayyana wani a matsayin wanda ya lashe zaben gaba daya,” inji Mista Soyebi.

“Ina matukar mika godiyata ga masu jefe kuri’a saboda mutunta dokokin zaben da suka yi, muna kuma godiya ga dukkan masu ruwa da tsaki musamman jam’iyyun siyasa da masu sa ido a kan yadda aka gudanar da zaben da jami’an tsaro da sarakunan gargajiya a bisa goyon baya da gudummawar da suka bamu a yayin da ake gudanar da zaben da kuma bayan kammala zaben gaba daya.

“Duk da haka lallai an samu nasara a gudanar da zabubkan, babban jami’in zaben, Farfesa Joseph Fuwape, shugaban jami’an Kimiyya da Fasaha na Akure, ya sanar da hukumar zabe INEC cewa, ya kasa sanar da wanda ya lashe zaben saboda rashin cika sharuddan da hukumar zaben ta gindaya a kan haka.

“Wannan yana faruwa ne saboda kasancewar wuraren da aka soke sakamakon zaben da kuma wuraren da rikici ya tashi, ya sanya ba a samu kammala zabe tare da samun sakamakon zaben ba.”

Ya kuma kara da cewa, za a sake gudanar da zabukkan ne a wurare da matsalar ta shafa tare da kasancewar dukkan jam’iyyu 48 da suka shiga zaben tun da farko.

“Sakamakon ya nuna cewa, banbancin dake tsakanin jam’iyyu biyu dake a kan gaba ya kai 353 wanda yake a kasa da mutanen da suka yi ragista a wararen da soke zaben ya shafa,” inji Mista Soyebi.

“Dokokin zabe sun nuna cewa, in har an samu irin wannan lamarin ba zai yiwu a sanar da wanda ya ci zabe ba, saboda haka hukumar ta zauna ta kuma tattauna inda aka yanke shawarar sake daura dammara da komawa fagen zabe a wuraren da lamarin ya shafa ranar 27 ga watan Satumba 2019 don sake gudanar da zabe da tattara sakamakon zaben da kuma sanar da duk wanda ya lashe zaben gaba daya.

“Muna kuma sanar da cewa, wannna zaben zai gudana ne kawai a wuraren da aka samu hatsaniya tare da soke zaben kawai wadanda suke guda 7, sun kuma hada ne da rumfar zabe 1 a karamar hukumar Ife North sai rumfar zabe 2 a karamar hukumar Ife South a karamar hukumar Orolu kuma a kwai rumfar zabe 3 sai rumfa 1 a karamar hukumar Osogbo”

Hukumar zabe ta kuma ce, an haramta gudanar da yakin neman zabe a tsakanin don kuwa tuni a ka dakatar da yakin neman zabe a ranar 21 ga watan satumba, don kuwa wannan zaben ci gaba ne ba wai wani sabon zabe a ka shirya ba.

Mista Soyebi ya kuma tabbatar da cewa, kuri’a ce kawai za ta tabbatar da gwamnan jihar Osun na gaba, babu wata hanyar da za a bi sai ta hanyar sake jefa kuri’a.

Jama’a na iya tunawa, dan takarar jam’iyyar PDP ya yi korafin canza alkalumar sakamakon zabe, a wata mazaba a karamar hukumar mai suna Ayedaade, inda aka canza alkalummar sakamakon zaben daga 10, 836 zuwa 9,836, wannan ya kara karfin korafin da jam’iyyun adawa ke yi na murdiya.

Dadewa da rashin kawo sakamakon zabe daga wasu kananan hukkumomi ya kara fargabar murdiyar zaben daga ‘yan adawa.

Jam’iyyar PDP ta nuna rashin amincewa da wannan shawarar amma ita kuwa jam’iyyar APC ta jinjina wa hukumar INEC a kan shawar, ta bukaci a yi kokarin gyara matsalolin da aka samu a zaben da za a sake na zagaye na biyu.

da sun samu budi a harkokinsu na yau da kullum.

Advertisement

labarai