KAYAN HADI:
1.Madaran gari rabin loka
2.Suga gwangwani biyu
- Leda
YADDA ZA A YI: A samu ruwa kamar rabin kofi a zuba a tukunya sai a juye suga, a bar shi ya yi ta dahuwa har sai ya yi kauri. In ki ka dan gwala za ki ga ya na yin danko kamar na aya, mai, suga.
Sai a juya bayan tire a shimfida leda a kwashe kafin ya fara yin brown, kada ki ce za ki bar shi bayan kin juya, ya na hadewa ki sauke. A samu mara ko muciya (kneading stick) a sa shi ya yi filat daidai kauri ko fadin da ki ke so. Shikenan sai a yayyanka shape din da a ke so.