TUWON MADARA

KAYAN HADI:

1.Madaran gari rabin loka

2.Suga gwangwani biyu

  1. Leda

YADDA ZA A YI: A samu ruwa kamar rabin kofi a zuba a tukunya sai a juye suga, a bar shi ya yi ta dahuwa har sai ya yi kauri. In ki ka dan gwala za ki ga ya na yin danko kamar na aya, mai, suga.

Sai ki dauko madarar ki na juyawa kina zubawa, idan ya shige duka shikenan in kuma bai shige ba sai ki bar sauran. Amma kada ya yi karfi sosai kada ki ce dole sai duka madararki ta shige.

Sai a juya bayan tire a shimfida leda a kwashe kafin ya fara yin brown, kada  ki ce za ki bar shi bayan kin juya, ya na hadewa ki sauke. A samu mara ko muciya (kneading stick) a sa shi ya yi filat daidai kauri ko fadin da ki ke so. Shikenan sai a yayyanka shape din da a ke so.

Exit mobile version