Connect with us

KIMIYYA

Twitter Ta Bukaci Masu Mu’amala Da Ita Da Su Canza Bayan Sirrinsu

Published

on

Kafar sada zumunta na Twitter ta sanar da masu mu’amala da ita su fiye da Miliyan 300 dasu gaggauta bayanan da suke amfani dasu bude shafinsu saboda a bisa kuskure kanfanin ya bayyana wa jama’a bayanan sirrin da masu mu’amala das u suke amfani dasu ta wani manhajar mai suna “Software bug”.

Kafar sada zumuntar ta Twiter, ta ce, duk da cewar, basu samu wani bayanin dake nuna masu satar bayanai sun yi amfani da bayyanan sirrin da aka yi ba , yana da kyau kowa ya canza bayanan sirririn domin kaucewa wata matsala.

Tsarin Twitter shi ne boye siriin masu mu’amala da ita ta yanda hatta ma’aikatan kanfanin basu da halin shiga domiun gano wadannan bayanan na masu amfani da kafar sada zumuntar, shugaban sashin kula da kimiyya na kanfanin, Mista Parag Agrawal ya yi wanan bayani a shafinsa na “blog post”.

“A saboda wata matsala mun rubuta bayanan sirin masu mu’amala damu a wani shafi kafin mu kamala sarrafa tsarin” inji shi.

“Mu da kanmu muka gano wannan matsalar, in nan take muka gyara, muna kokarin ganin irin haka bai sake faruwa ban a gaba”

Kafar sadarwar ta Twiter mai mazauni a garin San Francisco bai yi bayanin sirrin mutane nawa ne suka fito da kuma dadewar da bayanan suka yi kafin su gano abin daya faru.

“Saboda kaucewa wani matsala muna bukatar daku canza dukkn bayanan sirrin da kuke amfani dasu a sadar da zumuncin Twiter saboda fita daga duk wani matsakar da zai iya faruwa” a bayanin da Agrawal ya yi wa masu hulda dasu. “Muna baku hakuri a kana bin daya faru” inji shi.

Wannan matsala na zuwa ne a daidai lokacin da kanfanin ke fiuskantar bincike na musamman saboda tsarinsu na kare bayanan masu mu’amala dasu, tun bayan faruwar badakalar “Cambridge Analytica” data kai ga satar miliyoyin bayanan masu hulda da kafar sada zumunta na Facebook. A shekarar data gabata ne kanfanin Twitter ta sanar da samun gaggarumin riba abin daya daga darajarta a cikin ‘yan shekaru.

Kafar sada zumuntar ta samu Dala Miliyan 61 a cikin watani uku na farkon shekara, yawan masu mu’amala da ita da kuma tallan da ake samu ya karfafa mata samun wannan nasarar.

A zangon farko an samu karuwar kashi 21 na abin da aka samu  asjekarar data wuce zuwa Dala Miiyan 665 sannan an kuma samu karin masu amfani da kafar da mutum Miliyan 6 abin daya sa adadin suyka kai mutum Miliyan 336 a shekarar daya gabata.

Shugaban kafar sadarwa Mista Jack Dorsey ya ce, gyare gyare da aka gudanar a ‘yan kwanakin nan ya taimaka wajen rike jama’a masu mu’amala da kafar sadarwa. Duk da cewa, kafar Twiter na da masu mu’amala da ita daga bangarorin al’umma dabam dabam kamar ‘yan siysa da ‘yan jarida da sauran masu hannu da shuni amma har yanzu ta kasa fadada harkarta kamar kafar sadarwa ta Facebook, hakan kuma yana kawo mata cikasa wajen samun kudaden shiga daga masu bayar da tallace tallace.

Kanfain ya kara fito da wasu tsare tsare da zai karfafa masu mu’amala da ita, musamman ta hanyar karin yawan kalmomin da mutum zai iya amfani dasu wajen isar da sako zuwa 280 da kuma kirkiro da “tweetstorms” domin amfanar masu amfani da Twiter.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: