Tun bayan da shahararren dan wasan Dambe, Anthony Joshua, ya doke Kubrat Pulev dan kasar Bulgeriya a fafatawar da sukayi a tsakiyar watan daya gabata aka fara sa’insa ta maganganu tsakanin Anthony Joshua da Tyson Fury, wadanda ake ganin sune zasu kara da juna a wasan Dambe na gaba da za’a fafata a duniya a wannan shekarar.
Tyson Fury, dan Birtaniya, ya caccaki Anthony Joshua, wanda shima dan Birtaniyan ne inda ya bayyana shi a matsayin mai neman suna da Dambe kuma mai bayyana nasarorinsa a fili ba tare da bari duniya tana bayyanawa ba da kanta.
Duk da haka Fury ya bayyana cewa ya gama shiryawa tsaf domin doke Anthony Joshua a fafatawar tasu tan an gaba wadda ake saran zata kasance a wannan shekarar duk da cewa an sake saka sabuwar dokar kulle a Ingila amma dokar ba zata hana buga wasan ba.
Sai dai shima Anthony Joshua, ya bayyana cewa ya gama shiryawa domin fafata wasa da Tyson Fury, dan birtaniya, a wasan da zakarun biyu za su kece raini duk da cewa har yanzu ba’a saka ranar gwabzawar ba.
Tyson Fury, wanda shima ya shahara a duniya a fannin dambe ya ce cikin zagaye na uku gaba daya zai doke Joshua saboda shi har yanzu ba sa’ansa bane kuma yana da kwarin guiwar samun nasara akan matashin dan asalin Nigeriya.
A watan daya gabata ne Anthony Joshua ya doke Kubrat Pulev, dan asalin kasar Bulgeria wanda hakan ya kara fitowa da batun karawarsa da Tyson Fury fili kuma Joshua ya yi nasara ne a fafatawar da aka kai zagaye uku ana yi.
‘Yan kallo 1,000 ne dai aka bai wa damar shiga filin wasa na Wembley Arena, la’akari da daukar matakan bayar da tazara saboda annobar korona kuma jim kadan bayan nasarar da Anthony Joshua ya samu ne magoya bayansa suka rika fadar cewa ‘saura Fury’.
Furta hakan ke da wahala kuwa sai Anthony Joshua ya ba su amsar cewa ‘duk wanda ke da tarin kofuna ya zo na shirya’ kuma idan ma Tyson Fury ne, to shi ke nan a shirye yake ya kara da Tyson Fury’.
Ba da wata wata ba kuwa sai shima Tyson Fury ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa ‘to kun ji amsar Anthony Joshua game da karawa da ni kuma nima na shirya, na matsu na doke shi’ cikin zagaye uku kacal”.
‘Yan kallo 1,000 ne aka baiwa damar shiga filin wasa na Wembley Arena, la’akari da daukar matakan bada tazara saboda annobar Korona sai dain idan ba’a manta ba kadan ya rage ganiyar Joshua ta ruguje a watan Disambar bara, a lokacin da ya dauki fansa kan Andy Ruiz Jr.
Kuma kisan da ya yi wa Kubrat Pulev a fafatwar tasu ta nuna cewa a yanzu Tyson Fury ne kawai ya rage su saka zare, don ya tabbatar wa duniya kololuwar inda kwarewarsa ta kai a duniyar dambe.
Tuni Joshua ya fara shafar rayuwar samari da yawa musamman a kudu maso yammacin Najeriya, kamar Legas babban birnin kasuwancin kasar domin da yawa daga cikinsu sun kalli yadda ya zama shahararre ya cika burinsa na rayuwa, kuma labarinsa kusan yazo dai-dai da nasu, na wanda ya sha wahalar rayuwa kafin daga bisani kofar arzikinsa ta bude ya sha kwana.
Labarinsa, wani abu ne da aka jima ana nuna irinsa a fina-finai irin na Nollywood, kamar dai ace na mutumin da burinsa na rayuwa ya cika bayan shan kwarba shekara da shekaru sannan Joshua ya zama wata sila ta samun karvuwar harkar dambe a Najeriya, domin a yanzu, har ta kai ga ana horar da mutane wasan a makarantu bayan tashi daga karatu, da kuma ranakun hutu da sauran wurare da dama.
Duk da cewa tsarin da ake da shi na yin harkar ba wani na azo a gani bane, amma duk da haka kwarin guiwa na zaburar da matasa da dama sakamakon hakan nan gaba za’a iya samun ‘yan dambe masu yawa a kasar nan domin akwai matasa da dama irinsu Lekem duka suna sha’awar wasan.