UAE Ta Musanta Zargin Hana ‘Yan Nijeriya Biza

Ofishin jakadancin hadaddiyar daular Larabawa dake Nijeriya, ya musanta batun daina baiwa ‘yan Nijeriya shaidar bizar wata uku, ana rade-raden kasar ta daina baiwa ‘yan Nijeriya bizar wata ukun ne bayan da ake zargin wasu ‘yan asalin Nijeriya su biyar da aikata fashi a Dubai.

Ofishin jakadancin ya shaida hakan ne ta shafin sada zumuntar shi na Tuwita wato @UAEEmbassyNGR, bisa la’akari da wani rahoto da aka fitar a jiya Alhamis, inda ake zargin cewa kasar UAE din ta dakatar da baiwa ‘yan Nijeriya bizar wata uku da aka saba bayarwa a baya, ofishin jakadancin UAE da ke a Abuja, yana so ya shaida muku cewa wannan rahoton ba daidai bane.

Ofishin ya bainawa manema labarai cewar har yanzu tsarin bada bizar yana nan kamar yadda aka sani, don haka ofishin jakadancin ya bukaci da ayi watsi da wannan rahoton, inda ya bayyana shi a matsayin jita-jita, sannan ya bukaci duk masu neman sahihan bayanai daga ofishin, su bi hanyoyin da suka ace don samun bayanan.

Ana zargin wasu ‘yan asalin Nijeriya biyar sun afka wani babban shagon canjin Kudade, inda suka yi fashi, kwanaki kadan da afkuwar lamarin, wannan kamfanin tafiye-tafiye mai suna Africhoidays ya saki wani bayani, inda yake bayana cewa yanzu UAE ta dakatar da baiwa masu rike da fasfo din Nijeriya  bizar wata uku.

Exit mobile version