Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wani matashi mai suna Auwalu Awaisu dan shekara 19, bayan da mahaifinsa ya lakada masa duka tsiya a daren ranar Juma’a da ta gabata.
‘Yan sandan sun ce matashin ya mutu ne a ranar Litinin a Asibitin Murtala sakamakon dukan kawo wuka da mahaifin nasa ya yi masa a kai da kuma cikinsa.
A cewar ‘yan sandan, mahaifin Auwalu mai suna Awaisu Auwalu na zargin dan nasa Auwalu Awaisu da bata mishi da kudadensa.