Fasto Yohanna Y.D. Buru" />

Ubangiji Allah Makiyayi Ne A Garemu

WURIN KARATU – ZABURA 23:1

“Ubangiji Makiyayina ne; ba zan rasa komai ba” (Zebura 23:1)

Duk lokacin da aka ambaci makiyayi dole ne kankalin mutum ya kan karkata makiya kama Fulani. Amma anan, Sarki Dauda ya yi amfani da irin wannan misali da makiyayi domin shi makiyayin san a makiyayi yana sane da qaunar da ya ke da shi domin tumakinsa da kuma sadaxkarwan da yake da shi kuma da tumakinsa.

Domin tsananin qaunar da makiyayi ke yi wa tumakinsa har ya kan iya ya bada ransa domin ceton tumakinsa. A nan Sarki Dauda yana so ya nuna mana cewa Allah mai qaunar mu ne kuma shi mai iya yi komain ne domin biya mana buqatun mu da kuma cheton mu daga hallaka. Watau a nan Sarki Dauda na kara tabbatar mana da cewa, qaunar makiyayi a kan dabbobinsa bata da iyaka kuma yana sane da rauninsu.

Makiyayi na sane da haqqin tumakinsa akansa, watau tumakin amana ne a kansa domin da haka yana sane da haqqokin su a ansa. Domin haka ya zama wa makiyayi dole ne karesu da kuma biya masu buka tun zu.

To aininin maganan shi ne Allah ubangiji shi ne kaxai cikaken makiyayyi mu. Ubangiji makiyayin dukan Bil Adam kuma shi makiyayin dukan halittu. Shi ne kaxai makiyayi abubuwan duniya da na samai, kuma shi ne makiyayin dukkan abubuwan da ke aboye ko abayane. Dukan abubuwan da ka a sane ko ba a sani ba duk shi. Allah mahalimchi shi ne kaxai a cikaken makiyayin su duka.

Allah ubangiji makiyayin kowane irin al’unma ne kuma bai tava barrin kowane al’ummah haka nau ba tare da kiyayewansa ba. Domin kiyayewansa dukan al’ummai sun mayar da Allah ubangiji makiyayinsu da kuma madogaransu. Allah bai tava wata al’ummah ko guda xaya haka ba tare da kiyayewansa ba (Leviticus 27:17).

Yesu ubangiji ya kira kansa makiyayi maikyau, kama yadda zamu karanta da cewa.

“Nine makiyayi mai– Kyau: makiyayi mai – kyau yakan bada ransa domin tumaki” (Yohanna 10:11)

A chikin wannan ayar Yesu Almasihu ya kara tabbatar wa masu sauronsa da Almajiransa a lokacin daya ke magana cewa shi Yesu, shi ne makiyayi mai–kyau. Watau shi ba mugun makiyayi ba mai aiki lada ba ne (Yohanna 10:12). Domin shi mai aikin lada iyakan aikinsa shi ne ya yi aikinsa domin samu lada ne kaxai; amma cikaken makiyayi baya yin aikinsa domin karvan lada a’a.

Mai aikin lada ba zai tava yin tunanin bada ransa domin tumaki ba, amma a kwai bambanci tsakanin mai aikin lada da makiyayi mai kyau. Domin shi makiyayi mai kyau zai bada ransa domin tumakinsa a kan tsnanin qaunar da yake dashi a kan tunakinsa. Amma ga mai aikin lada baya ko tunani na kuskure na bada ransa domin tumaki dalilin da mai aikin lada baya tunanin ya bada ransa domin tumakin shi ne domin na farko; tumaki ba nasa bane kuma baya qaunar tumakin iyaka ladansa ne kaxai yake buqata.

A kwai abin da ya kuma bambanta makiyayi mai– kyau da mai aikin lada kama yadda zamu karanta da cewa.

“Ni ne makiyayi mai – kyau; na san nawa kuma sun san ni” (Yohanna 10:14).

Bambancin da ke tsakanin makiyayi mai–kyau da mai aikin lada shi ne makiyayi mai-kyau na sane da duka tumainsa domin nasa ne amma mai-aikin lada bai damu ba, domin tumakin ba nasa bane. Iyakan abinda shi mai aikin lada ya sani shi ne ladansa ne kawai. Sanin da ke tsakanin makiyayi mai-kyau da tumakinsa cikaken sani ne. domin tsananin sanin da ke tsakanin makiyayi mai-kyau da tumakinsa har tumakin sun san da muryar makiyayi mai-kyau kumma su ka iya bambanta muryan makiyayi mai-kyau da bakon mutum. Yesu Almasihu ya ci gaba da cewa.

“Tumakin suna jin muryaya, na kwa san su, suna biyona Kuma” (Yohanna 10:27).

A nan Yesu Almasihu ya qara tabbatar mana da cewa fa dukan tumakinsa suna sane da muryansa kuma suna jin muryansa tawurin iya bambanta muryansa da na kowane irin mutum. A matsayinsa na makiyayin sun a gaskiya su tumakin su kan ji muryarsa su kuma bishi basu bin wanda basu sani ba.

Wato kowane baqon murya su tumakin ubangiji sun sani kuma sukan bambanta shi baicin bambanta was u ka guji bakon mutum. Amma su kan gane da muryan makiyayi mai-kyau su kuma bishi domin suna sane da cewa shi ne tudun muntsiransu.

To jama’a in dabba watau tumaki sun a sane da makiyayinsu na mai-kyau kuma makiyayinsu na gaskiya. To ashe ya kamata masu bi na gaskiya ya kamata su san da makiyayinsu na gaskiya kuma su bishi na gaskiya. Yadda makiyayi na sane da tumakinsa hakane tumakin na sane dashi makiyayinsu na gaskiya.

Domin da haka, ya kamata kowane Krista na gaskiya ya san da cewa Allah ubangijimu na sane da dukan mu da kuma duka bulatunmu ko na jiki da na ruhaniya. Allah ubangiji na sane da mu kuma ya damau da mu domin mu tumakinsa ne. yana qaunanmu domin shi ne ya halicemu kuma shi ne cikakken makiyayinmu mai– kyau kuma shi ne mai qaunarmu.

Allah shi ne kai xai ke da qauna na gaskiya domin mu kuma shi ne kaxai ke da ikon da zai kare mu a chikin kowane hali da muka sani kan mu. Domin da haka ya kamata mu sani da cewa Yesu ubangiji shi ne cikaken makiyayi mai-kyau kuma shine kaxai zai iya bada ransa domin cetonmu ko fansanmu. In kuwa ubangiji Allah shi ne makiyayinmu mai–kyau to, ashe ba zamu tabba rasa komai ba. A matsayinsa na makiyayinmu to shi ne kaxai maibiya mana dukan buqatunmu. Domin da haka bari kowane mutum ya mayar da Allah kaxai ma dogaransa.

Shalom !  Shalom !!  Shalom!!!

Exit mobile version