Hukumar kula da kwallon Kafa ta nahiyar turai, EUFA ta fara binciken hatsaniyar da aka samu a kofar shiga filin wasa na Emirate a wasan da Arsenal ta fafata da FC Koln a gasar cin kofin Europa da aka fafata a ranar Alhamis.
An dai yi zargin cewa magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta FC Koln ne suka tayar da tarzoma sakamakon hana su shiga filin wasan.
Kungiyar Arsenal dai ta warewa magoya bayan FC Koln tikitin shiga wasan guda dubu uku, amma wadanda suka halarta a bakin shiga filin wasan sun kai mutum dubu goma sha biyar, wanda hakan ya haifar da tarzoma sakamakon yunkurin da magoya bayan da suka yi na cewa dole sai sun shiga filin wasan.
Itama kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta ce ta fara binciken abinda ya faru, kuma za ta dauki mataki akan duk wanda aka kama, inda ta ce tana aiki tare da jami’an hukumar UEFA da na kungiyar FC koln don ganin an dauki mataki.
Rahotanni dai sun ce an kama mutane biyar wadanda ake zargin suna da hannu wajen tayar da hargitsin.