UEFA Za Ta Hukunta Kungiyoyin Celtic Da PSG

Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai ta ce zata dauki mataki mai tsauri kan kungiyar kwallon kafa ta Celtic, biyo bayan bayan kundunbalar da daya daga cikin magoya bayan kungiyar yayi cikin fili, yayinda suke fafata wasa tsakaninsu da PSG wato Paris Saint German a ranar Talatar da ta gabata.

Magoyin bayan Cetltic din yayi kan Kylian Mbappe da niyyar kirba masa kafa, jim kadan bayanda PSG ta zura kwallo ta 3 a ragar Celtic din a wasan na jiya da suka lallasa su da kawallaye 5-0.

A gefe guda kuma hukumar ta UEFA, ta ce zata hukunta kungiyar PSG, ita kuma lafinta, shi ne lalata wasu kujeru da magoya bayanta suka yi, yayin fafatawar da suka yi a wasan na jiya a filin wasan na Celtic.

UEFA ta ce sai a ranar 19 ga watan Oktoba mai zuwa, kwamitin da’arta zai tantance hukuncin da zai yankewa kungiyoyin na Celtic da PSG.

Mutane 7 ‘yan sandan Scotland suka kame saboda aikata laifuka yayin wasan ranar Talatar.

Exit mobile version