Abba Ibrahim Wada" />

UFDD Ta Nemi Gwamnati Ta Sa Hannu Wurin Nemo Dadiyata

Wata kungiya mai rajin tabbatar da dimokradiyya a kasar nan wadda take zaune a jihar Kano mai suna United Front For The Debelopment Of Democracy (UFDD) tayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari akan yayi kokarin ganin angano inda Abubakar Idris, wanda akafi sani da Dadiyata yake wanda wasu mutane suka daukeshi tun ranar 2 ga watan Agustan wannan shekarar, wato yau kwana 82 kenan har yanzu ba’a samu labarin inda yake ba.

kungiyar, tayi wannan kira ne a wani taron manema labarai data kira a jiya Talata a jihar Kano inda kuma shugaban kungiyar, Isma’il Auwal, ya bayyana cewa suna kira ga jami’an tsaro da gwamnatin tarayya da kuma bangaren kwankwasiyya dasu tashi tsaye domin ganin Abubakar Daniya ta ya koma cikin iyalansa cikin koshin lafiya.

Tun bayan da wasu wadanda ba’asan ko suwaye ba sukaje har gida suka tafi da Dadiyata har yanzu ba’asan halin da yake ciki ba kuma a kwanakin baya mahaifin Dadiyata yayi kira ga gwamnati akan cewa tayi kokari wajen ganin andawo masa da dansa.

“Muna kira ga gwamnatin tarayya da tayi kokari wajen gano dan uwanmu matashi wato Abubakar Idris Dadiyata sannan kuma muna kira ga jami’an tsaro akan suyi iya yinsu domin ganin Abubakar ya dawo gida” in ji Isma’il

Ya cigaba da cewa “Shima shugaban darikar kwankwasiyya, Dr Rabiu Musa Kwankwaso muna kira da yafito ya jajantawa iyalan Dadiyata saboda har yanzu bamuji wata sanarwa wadda take bayyana cewa Kwankwaso ya jajantawa iyalansa ba kuma muna kira a gareshi day adage wajen ganin an samu labarin inda wannan matashi yake”

Ismail ya kara da cewa idan duka matakan da suka dauka akan Dadiyata basu samar da abinda ake bukata ba za suyi kira ga ‘yan Najeriya dasu fito kwansu da kwarkwatarsu domin yin jerin gwano a ofisoshin jami’an tsaro akan cewa lallai sai an bayyanawa ‘yan Nijeriya inda Dadiyata yake.

Abubakar Idris Dadiyata dai malamine a jami’ar gwamnatin tarayya dake Dutsinma jihar Jigawa kuma ya kasance yana yawan rubuce-rubuce domin kare tafiyar kwankwasiyya da jam’iyyar PDP sannan kuma mazaunin jihar Kaduna ne.

Exit mobile version