Uganda Na Son Yi Wa Dokar Tsayawa Takara Garambawul

Jam’iyya mai mulki a Uganda na yunkurin gabatar da wata doka a zauren majalisar kasar wadda za ta soke adadin shekarun da aka kayyade wa mutun kafin cancantar tsayawa takarar shugaban kasa.

Kundin tsarin mulkin Uganda ya haramta wa mutumin da ya zarce shekaru 75 tsayawa takarar shugabancin kasa, yayin da jam’iyyar shugaba Yoweri Musebeni mai shekaru 73 da haihuwa ke bukatar yi wa dokar kwaskwarima.

Ana ganin cewa, jam’iyyar ta dauki wannan matakinne don bai wa shugaba Musebeni damar neman wani sabon wa’adi nan gaba.

Simeo Nsubuga, dan majalisa daga Jam’iyyar National Resistence Mobement ta Musebeni ya ce tuni suka amince da shirin a taron jam’iyyarsu.

Exit mobile version