Connect with us

KASASHEN WAJE

Uganda Na Tuhumar Wani Dan Adawa Da Laifin Cin Amanar Kasa

Published

on

Wani dan majalisar dokokin kasar Uganda na bangaren ‘yan adawa, wanda asalinsa fitaccen mawaki ne, na fuskantar tuhuma kan laifin cin amanar kasa, bayan da hukumomi suka yi watsi da wata tuhuma da ake masa kan wasu makamai.
Robert Kyagulanyi, wanda aka fi sani da Bobi Wine a harkar waka, ya bayyana ne a gaban wata kotun soji a jiya a arewacin garin Gulu, domin fuskantar tuhumar da ake masa kan makaman.
Kotun dai ta yi watsi da cajin, amma kuma nan take ‘yan sanda suka sake tsare shi, inda aka shigar da wata sabuwar tuhuma akansa, ta cin amanar kasa.
Alkalin kotun ya sa a tsare dan majalisar a gidan wakafi, har sai ranar 30 ga watan nan na Agusta.
A makon da ya gabata aka kama Kyagulanyi tare da wasu ‘yan majalisa hudu, inda ake zarginsu da hannu a wani hari da aka kai akan jerin gwanon motocin shugaba Yoweri Musebeni a garin Arua.
Akwai zargin cewa masu zanga zanga sun yi wa ayarin motocin na Musebeni Shewa tare da jifansa da duwatsu, a lokacin yana kyamfe a zaben maye gurbin wani dan majalisar yanki.
A lokacin, Kyagulanyi, yana yankin a yana yi wa wani dan takara a bangaren ‘yan adawa kyamfe.
Advertisement

labarai