Uhuru Kenyatta Ya Lashe Zaɓen Kenya

Shugaban Hukumar Zaben Kenya, Wafula Chebukati ya bayyana shugaba Uhuru Kenyatta a matsayin wanda ya lashe zaben kasar da kuri’u sama da kashi 98 bayan janyewar ‘yan adawa.

Bayanai sun ce kashi kusan 39 na masu kada kuri’u suka shiga zaben, kuma Kenyatta ya samu kuri’u miliyan 7 da 483,895.

Zaben Kenya ya jefa kasar cikin rikicin tsawon watanni biyu bayan kotun koli ta soke zaben da ya bai wa Kenyatta nasaran farko a ranar 8 ga Watan Agusta.

Chebukati da ya bayanan shaku kan sahihanci maimacin zaben ya tabbatar da ingancin sakamakon na wannan lokaci.

 

Exit mobile version