Abdulazeez Kabir Muhammad" />

Ukraine Ta Lashe Kofin Duniya Na ‘Yan Kasa Da Shekara 20

A jiya Asabar ne aka buga wasan karshe na kofin duniya na yan kasa da shekara 20 tsakanin kasar Ukraine Da Korea Republic wanda aka filin wasan na Lodz dake kasar Poland inda kasar Ukraine ta doke Korea da ci uku da daya.

Korea ce ta fara jefa kwallo ta hannun dan wasan ta Lee Kangin a bugun daga kai sai mai tsaron raga a minti biyar da fara wasan.

Dan wasa Vladyslav Supriaha ya jefa wa Ukraine kwallon farko a minti 34 kafin daga bisani ya jefa kwallo ta biyu a minti takwas da dawo wa daga hutun rabin lokaci. Heorhii Tsitaishvili ya jefa wa Ukaraine kwallo ta uku a minti na 89.

Exit mobile version