Umurnin CGI Babandede Ga Jami’an NIS: Ku Kiyaye Hakkin ‘Yan Kasa Da Tsare Mutuncin Kanku

Babandede

Daga Abdulrazak Yahuza Jere

Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa, CGI Muhammad Babandede MFR ya umurci jami’an hukumar su guji aikata duk wani abin kunya na muzguna wa jama’a ko shiga cikin masu sace-sacen kaya bisa la’akari da yanayin da ake ciki a kasa, kasancewar su jami’ai ne masu aiki a bangaren kare mutunci da martabar kasa.

Shugaban na NIS, ya bayar da umurnin ne a yayin gudanar da faretin kwanturola janar na watan Oktoba. Inda ya bukaci jami’an su kiyaye hakkin ‘yan kasa nagari masu bin doka da ke shige da ficen kasa ta hanyar tabbatar da cewa ba a tatsi ko kwabo daga matafiyin da ya cike ka’idar tafiye-tafiye zuwa waje ba.

CGI Babandede ya kuma jaddada cewa tafiya zuwa kasar waje ba aba ce da ta zama dalilin tatsar wani mutum kudi ba; baya ga kudin ka’ida da aka sa, shi ma ta shafin intanet aka ce a biya saboda tsarin biza na nan take. Wannan din shi ma bai shafi mutanen da kasashensu ke cikin Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Yammacin Afirka ta ECOWAS ba da aka tsame su daga cikin wadanda za su biya kudi yayin da suke shiga daya daga cikin kasashen kungiyar. Sai dai su sharadi ne a kansu su tabbatar sun mallaki sahihan takardun izinin tafiye-tafiye kuma su biyo ta mashigin da aka amince a shigo kasa ta shi; ba ta barauniyar hanya ba.

Sanarwar da ta fito daga Jami’in yada labarun NIS, DCI James Sunday, ta kara da cewa, CGI Muhammad Babandede ya tabbatar da cewa a matsayin hukumar ta jagaba a fannin difilomasiyyar ‘yan kasa; a koyaushe za ta tabbatar da ana girmama ‘Yan Nijeriya a yayin hulda da ita, ba ma su kadai ba har ma da ‘yan wasu kasashen.

Wakazalika sanarwar ta ce hukumar za ta yi wani kwarya-kwaryar gyaran fuska ta hanyar daidaita mukaman jami’anta da suka dace sakamakon soke bambancin da ke tsakanin wanda ya yi karatun Digiri da na HND, wanda Shugaban na NIS ya ce abu ne da ya dace.

Dama dai CGI Babandede a koyaushe yana fatan ganin ana muhimmanta jami’ai masu kwarewar aiki a maimakon masu aiki da takardar shaidar karatu kawai da ba su da kwarewa.

Sanarwar ta karkare da cewa da dama daga cikin jami’an hukumar da suke bangaren insifekta za su sanya sababbin mukamansu da suka dace da su, kasancewar jijiyon wuyar da ake tayarwa kan bambanta mai Digiri da HND zai zama tarihi.

 

Exit mobile version