Hukumar raya ilimi kimiyya da al’adu ta MDD UNESCO, ta sanya wasan Taijiquan da ake yi a kasar Sin, cikin jerin al’adu da aka gada daga kaka da kakanni wadanda ba na kayayyaki ba.
A ranar Alhamis ta makon jiya ne dai UNESCO ta sanar da hakan, yayin taro ta kafar bidiyo dake gudana, karkashin lemar kwamitin hadin gwiwar gwamnatoci, game da kare al’adun da aka gada daga kaka da kakanni wadanda ba na kayayyaki.
Taijiquan, wasa ne na gargajiya mai kunshe da salon fada da kare kai, wanda ya samo asali tun cikin tsakiyar karni na 17, daga wani karamin kauye da ake kira da Chenjiagou, wanda ke lardin Henan na tsakiyar kasar Sin. Daga bisani ya bazu zuwa sama da kasashe da yankuna 150 a sassan duniya daban daban. Ya zuwa yanzu, mutane sama da miliyan 100 na yin wannan wasa.
Taron na wannan karo dai na gudana ne tsakanin ranekun 14 zuwa 19 ga watan nan na Disamba a birnin Kingston, fadar mulkin kasar Jamaica. (Mai fassara: Saminu Hassan)