Unguwannin Kano Da Suka Shafe Shekaru 30 Ba Ruwan Famfo Yanzu Sun Samu – Dr. Kofar Wambai

famfo

 Daga Ibrahim Muhammad

 

Shugaban hukumar bada ruwan sha na jihar Kano, Dr. Garba Ahmad Kofar Wambai ya  bayyana cewa sun sami nasarar tura ruwa wasu unguwannin a cikin kwaryar kananan hukumomin Birnin  jihar Kano da suka shafe kusan shekaru 30 rabon su da samun ruwan fanfo, tun daga lokacin da ya zama shugaban hukumar.

Ya bayyana haka ne a wajen taron bikin bayyana irin nasarorin da ya samu a kokarinsa na samar da wadataccen tsaftataccen ruwansha ga al’ummar jihar ta sauke nauyin da Gwamna Ganduje ya dora masa.

Ya bayyana cewa, daga Unguwannin da ruwan ya samu har da Unguwanin Nasarawa GRA da sauran wurare hakan ya samu ne kuwa sakamakon gyararraki da a ka yi a matatar ruwa na Chalawa da Tamburawa.

Ya ce a lokacin da ya zo akwai karancin wasu kayayyakin aiki a matatun da a ke da bukatarsu, ya zo ya kara yawancinsu domin bunkasa harkar samar da ruwansha.

Dokta Garba Ahmad Kofar Wambai ya ce akwai ma’ajiyar ruwa ta Magwan da ta jima ba’a tura mata ruwa amma zuwansa duk da hatsarin wajen na macizai haka suka shiga don gyarawa hakan zai taimakawa samar da ruwa.

Ya ce, yanzu haka akwai ayyukan cire tsofaffin bututun ruwa da su ke shinfide da suka  toshe  a domin a sanya sabbi domin ruwa ya rika zuwa inda yakamata.

Dokta Garba Ahmad Kofar wambai ya bayyana matukar godiya ga Gwamnan Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje bisa kulawa da ya ke baiwa hukumar. Sannan kuma ya yi kira da a samawa lalitarsu kudade masu yawa da za su cigaba da gudanar da dinbin ayyukan da ke a gabansu wanda yanzu haka kuma lalitarsu tayi karkaf.

Ya ce idan a ka yi ayyuka a hukumar bada ruwan zai taimaka wajen samar da kudin shiga ta wadata al’umma da dama.

Ya kuma godewa kwamishinan ma’aikatar ruwa na jihar Kano.Alhaji Sadik Wali bisa hadin-kai da ya ke basu tareda godewa dukkan ma’aikatar hukumar  bisa jajircewarsu da yin aiki tukuru.

A jawabinsa babban sakatare a ma’aikatar ruwa ta Kano.Dokta Usaini Umar Ganduje ya yabawa kwazon manajan daraktan hukumar ruwanshan a bisa jajircrwarsa don ganin an sami wadataccen ruwa a Kano.

A yayin taron an raba takardun karramawa ga wasu da ke bada gudummuwa domin samun nasarar hukumar, an kuma rarraba kayan aiki ga ma’aikatan hukumar.

Sai dai duk da cewa hukumar bada ruwanshan na bayyana nasarori da ya ke samu wajen raba ruwa har yanzu wasu dinbin unguwanni na kukan wahalar ruwa da su ke fuskanta a kwaryar birnin Kano.

 

Exit mobile version