Asusun kula da kananan yara ta Majalisar dinkin Duniya (UNICEF) reshen ofishinsu da ke Bauchi ya shaida a jiya cewa ya gyara tare da yin kwaskwarima wa cibiyoyin kula da lafiyan jama’a a matakin farko (PHCs) guda 104 tare da hannantasu ga gwamnatin jihar Bauchi domin cigaba da kula da lafiyar al’umman jihar.
Da ya ke mika gyararren cibiyar kula da lafiya ta zamani da suka samar a kauyen Yalwan Duguri da ke cikin karamar hukumar Alkaleri a jiya, Babban jami’in UNICEF a Bauchi, Mista Bahnu Pathak, ya shaida cewar UNICEF baya ga wannan sun kuma samar da kayayyakin aiki ga kananan cibiyoyin lafiya 323 da suke fadin jihar dukka a kokarinsu na taimaka wa gwamnatin jihar wajen kula da lafiya yadda ya dace.
Ya shaida cewar asusun nasu na aiki kafada da kafada da ma’aikatar lafiya ta jihar gami da hukumar lafiya a matakin farko ta jihar domin tabbatar da samar da kula da kiwon lafiya mai inganci da nagarta ga jama’an jihar, yana mai karawa da cewa cibiyar kula da lafiya da suka gyara a Duguri na daga cikin muhimman cibiyoyi na zamani da aka samar domin kula da lafiyar dumbin jama’a cikin salo na zamani.
Daga bisani ya roki gwamnatin jihar, al’umman yankin da aka samar musu da asibitin zamanin da cewa su yi wa Allah su kula da cibiyar domin daurewarsa, “Mu dai mun yi namu, don haka muna rokon jami’an lafiya da jama’an wannan yankin da su taimaka su kiyaye wannan cibiya da kayan da suke ciki domin tabbatar da an ci gajiyarsa tsawon lokaci,” ya roka.
Babban jami’in ya kuma shaida cewar UNICEF na aikin hadin guiwa da gidauniyar Bill and Millenda Gates Foundation, da kuma Dangote Foundation wajen taimaka wa gwamnatin jihar ta fuskacin cika alkawuran da ta dauka, ya kuma ce suna taimaka wajen rage yawaitar mace-macen kananan yara ta fuskakokin da suka dace.
Da ya ke amsar cibiyar da aka gyaran, shugaban hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar Bauchi, Rilwanu Muhammad, ya shaida cewar tsawon shekaru cibiyar ya kasance cikin halin kakanikayi, yana mai cewa a bisa kokarin gwamnati mai ci ana ta samun shawo kan matsalolin da suke akwai a cibiyoyin kula da lafiya da suke fadin jihar, daga nan sai ya nuna cewa nan kusa kadan za a samu fito da sabbin tsare-tsaren kyautata wa ma’aikatan lafiya rayuwarsu domin su ma su cigaba da bada gudunmawa ta fuskacin kula da lafiyar jama’a.
Ya gargadi jami’an lafiya da cewa suke tsayuwa a fagen aikinsu bisa gaskiya a daidai lokacin da ya basu tabbacin himmar gwamnati na kyautata musu jin dadi da walwalarsu domin samun yin aiki yadda ya dace.
Rilwanu wanda shine ya wakilci kwamishinan lafiya na jihar Dakta Aliyu Maigoro, ya nuna cewa tabbbas UNICEF suna matukar taimakawa gwamnatin jihar wajen sauke nauyin kula da lafiyar jama’an jihar.
Shi ma dai ya roki jama’a da su maida hankali wajen kula da cibiyar da aka samar, yana mai cewa gwamnatin ta maida hankali wajen shawo kan yawaitar mace-macen yara da iyaye a fagen haihuwa.
Dakarun Tsaro Sun Dakatar Da Aiki A Yankin Orlu Na Jihar Imo
Daga Rabiu Ali Indabawa, A wani labarin kuma, Dakarun sun...