United Na Zawarcin Ozil

Fitaccen ɗan wasan ƙungiyar Arsenal kuma ɗan asalin ƙasar Jamus Mas’ud Ozil, a halin yanzu ƙungiyar Manchester United ce zawarcinsa. Ozil wanda har yanzu bai sake kwantaragi a arsenal ba, kuma wanda hakan yake nuni da cewa ɗan wasan bashi da niyyar zama a ƙungiyar idan kakar wasa ta ƙare.

Sai dai tuni ƙungiyoyi suka fara zawarcin ɗan wasan, inda a baya-bayan nan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester united ce akan gaba a masu zawarcin ɗan wasan.

Amma ƙungiyoyin Inter Millan da Fernabahce tuni suka ƙagu wajen ganin ɗan wasan ya koma ƙungiyoyin na su. ko a baya-bayan nan ma sai da shugaban gudanarwar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Inter Milan ya bayyana aniyarsa ta ɗaukar ɗan wasan.

Amma rahotanni sun bayyana cewa ɗan wasan yafi son yaci gaba da buga wasanninsa a gasar firimiya ta Ingila ko kuma gasar Laliga ta Spaniya, duk da cewa a baya ya buga a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid.

An ruwaito cewa ɗan wasan ya fi son komawa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United ƙarƙashin jagorancin Jose Mourinho tunda daman sun yi aiki tare a Real Madrid daga shekara ta 2010 zuwa shekara ta 2013.

Har ila yau ɗan wasa yana da sha’awar buga wasa a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona sai dai an bayyana cewa Barcelona za su neme shi ne in dai har suka kasa samun Coutinho daga Liɓerpool a kakar wasa mai zuwa.

Ozil dai har yanzu a wannan kakar bai zura ƙwallo a raga ba sannna, kuma bai taimaka anci ba cikin wasanni biyar da ya buga a ƙungiyar Arsenal.

Exit mobile version