USAID Da NESTLE Sun Horar Da Manoma Da Malaman Gona Dabarun Zamani

Tumatir

Fannin ci gaban kasa da kasa na kasar amurka USAID da wasu kungiyoyi guda uku daga yanzu zasu dinga horar da manoma da malaman gona akan matsakaitun aikin gona da harkar kasuwanci a jihar.

Hakan yana kunshe ne a cikin sanarwar da kungiyoyin suka sanyawa hannu suka kuma raba manema labarai.

Sauran kungiyoyin uku sune, kamfanin Nestlé da kungiyar sa kai ta inganta tattalin arzikin kasa da kuma kungiyar BEGA.

Kungiyoyin zasu dinga gudanar da shirin ne a karkashin sabuwar hadaka ta mai taken,” ciyar da kasa abinci da masarar Nestlé mai karko don inganta hadin gwaiwa.”

Taron yana mahimmancin gaske kasancewar yin girbi na farko, ana samun asara da kuma sauran kalubale da ake fuskanta na amfanin gona kamar na waken soya da masara da ke zamowa matsala ga kananan manoma har su kasa samun wani jarin azo a gani.

Gurbatar amfanin gona, yana shafar lafiyar alumma harda da rayukansu da kuma lafiyar dabbobi, inda hakan ke janyo ciwon cutar daji data koda da liba.

Sanarwar taci gaba da cewa,I hakan na kuma shafar lafiyar yara, kamar shafar girmansu da kuma sanya masu cututtuka.

Sun bayyana cewa, manoman zasu koyi ilimin yadda zasu magance gurbacewar amfanin na gona don samar da ingantacciyar masara da waken soya da zasu karawa alummar kasar nan lafiya.

A kan hadin gwaiwar, Darakta a USAID Stephen Haykin, ya sanar da cewa, hadakar tsakanin masa’antu masu zaman kansu da bangaren gwamnati zai taimaka wajen ragewa manoman talauci ta hanyar koyar dasu dabarun noma na zamani da kuma samar masu da kudin shiga, inda ya kara da cewa horarwar kuma zata basu ilimi wajen inganta amfanin gonar su.

Shi ma a nashi jawabin, Manajin  Darakata na kamfanin Nestlé Mista Mauricio Alarcon, ya ce, hadakar anyi ta ne a bisa ka’idojin kamfanin musamman don inganta lafiyar ‘yan baya, inda ya yi nuni da cewa, “a yau a cikin gida ana samar da kayayyakin sarrfawa sama da kashi 80 bisa dari, kuma a shirye muke da mu kara habaka hakan a kasar nan.”

Ya cigaba cewa, “mun yi imanin cewar hadakar da alumma da kungiyoyin  zata taimaka wajen inganta rayuwar alumma da suka suka shafi ayyukanmu.”

Shi ma shugaban kungiyar CNFA kuma babban jami’i Sylbain Roy ya bayyana cewar hadakar zata taimkawa kungiyar tasu, wajen samar da kwararru don taimakawa kananan manoman dake daukacin fadin duniya, ya kara da cewa, kungiyar tasu a shirye take wajen ganin ta samar da canji mai amfani.

Haka shi ma shugaba kuma jami’i a kungiyar BEGA Michael Deal ya nuna jin dadinsa a bisa hadakar, inda y ace hadakar zata samar da mafita da ci gaba ga kananan manoma dake kasar nan da kuma iyalial.

A karshe ya bada tabbacicn cewra, kungiyar tasu zata ci gaba da tabbatar da hadakar musamman don a samu sakamako mai amfani.

Exit mobile version