Yusuf Abdullahi Yakasai" />

USAID Ta Karrama Dan Jihar Nasarawa A Kan Zaman Lafiya  

Hukumar da ke kula da sashen bunkasa ci gaban kasashen duniya ta Amurka (USAID) ta karrama wani dan asalin Jihar Nasarawa, Alhaji Osabo Mohammed Ahmed saboda jaruntakarsa wajen tabbatar da zaman lafiya da hadin kan al’uma.

Hukumar ta nunar da cewa saboda kokarinsa wajen ganin an samu zaman lafiya a tsakanin manoma da makiyaya ta ga ya cancanta ta bashi wannan lambar girmamawa da yabo da karrama shi.

Alhaji Osabo Mohammed Ahmed dai ya taba rike matsayin shugaban karamar hukumar Obi da karamar hukumar Lafiya duk a cikin Jihar Nasarawa. Haka nan ya rike mukamai daban-daban a jihar, inda ya rika ba da  shawarwari don ci gaban jihar tasa.

A takaitaccen jawabin da ya yi, Alhaji Osabo Mohammed Ahmed ya nuna farin cikinsa da jindadi saboda wannan karrama shi da aka yi, yana mai cewa, “Ina godiya gare su bisa wannan karramawa, sannan ina kara yaba wa kyakkyawar dangantakar da ke tsakain Nijeriya da Amurka. Allah ya ba mu zaman lafiya bakidaya a Nijeriya da kuma duniya,” in ji shi.

 

Exit mobile version