Connect with us

LABARAI

UTME: Kashi 25 Ne Kadai Suka Ci Sama Da Maki 200, Inji Oloyede

Published

on

Magatakardan hukumar shirya jarabawar shiga Jami’a, Farfesa Ishak Oloyede, ya ce, dalibai 414,696 cikin dalibai 1,603,181, da suka rubuta jarabawar shiga manyan makarantun kasar nan a wannan shekarar ta 2018 ne kadai suka sami cin sama da maki 200.

A cewarsa, hakan ya nuna kashi 25.09 kenan na daliban.

Wannan kuma ya saba wa, 465,025 (kashi 27.00) na dalibai 1, 606, 374 da suka sami sama da maki 200 a 2017.

Shugaban na JAMB, ya ce, dalibai 558, 673 sun ci sama da maki 190; 739, 490 sun sami sama da maki 180, sannan, 956, 937 suka sami sama da maki 170.

Ya bayyana duk hakan ne ranar Talata wajen kaddamar da sabon makeken dakin taro na, Bola Babalakin, wanda aka yi a Gbongan, ta Jihar Osun.

Dakin taron yana da girman da zai iya daukan mutane 2,400, shugaban kamfanin, ‘Bi-Courtney Group of Companies, Dakta Wale Babalakin, ne ya gina shi.

Bikin ya sami halartar Gwamnan Jihar Ogbeni Rauf Aregbesola, da kuma Ministan Ilimi, Adamu Adamu, da sauran manyan masu fada a ji a harkar Ilimi, sai dai kuma, Oloyede, din ya yi gargadin cewa, wannan sakanakon da hukumar ta JAMB ta bayar ba shi ne na yawan makin da aka rage ba.

Ya kara da cewa, “Kowane dalibi yana da daman ya amsa ko ya ki amsan gurbin karatun da aka ba shi, kafin a kammala gudanar da shirin.

“A yanzun dalibai suna da daman kin karban guraban karatun da aka ba su, in har suna jin ba a yi masu adalci ba.”

Da yake na shi jawabin, Ministan Ilimin, Adamu Adamu, ya bukaci hukumomin manyan makarantun ne da su himmantu tare da hukumar ta JAMB domin tsarkake hanyoyin shiga manyan makarantun a kasar nan.

 
Advertisement

labarai