Sani Hamisu" />

Uwa Ta Taimaka Wa Danta Kashe Mahaifinsa A Neja

Yan sanda sun yi nasarar kama Hafsat Aliyu mai kimanin shekaru 50, a duniya da kuma dan ta Babangida Usman bisa zargin su da ake na kashe Ali Haruna har lahira.
Wannan lamarin ya faru ne a ranar 13 ga Afrilu, 2019, a bayan makarantar firamare ta Shango a lardin Chanchaga na jihar Neja.
Rahotannin sun nuna cewa Babangida da mahaifiyar sa sun yi nasarar kashe Ali ne lokacin da suka samu matsala tsakin su.
A cewarsa, Babangida” mahaifina ne yayi kokarin kashe mahaifiya ta to ni kuma a daidai lokacin sai nayi kokarin hanawa amma a cikin kokarin da nake ban san lokacin da ya mutu ba. “
Ya ce, “Uwata basa jituwa kullum da mahaifina sabida kullum suna cikin fada tsakanin su a lokacin da suke dokan sa ba muyi tunanin cewa zai mutu ba kawai nide na shiga fadan ne saboda na kare mahaifiya daga dukan sa.”
Kakakin rundunar jihar Neja Mohammed Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce wadanda ake zargi da laifin aikata kisan yanzu suna hannun hukuma.
Abubakar ya ce “Usman da mahaifiyarsa kafin su kashe marigayin sai da suka masa mummunan raunuka a jikin sa, wanda yayi sanadiyyar mutuwar sa tun kafin a kai sa Asibiti.
Ya kara da cewa “Wadanda ake zargi da aikata laifin za a gurfanar da su a gaban kotu domin a yanke musu hukuncin da yayi daidai da su”.

Exit mobile version