Daga Mustapha Hamid
Tsohon Shugaban ƙasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida, jiya a gidansa da ke kan tsauni a garin Minna ya gargaɗi ‘yan siyasa da su kiyayi yin amfani da siyasa wurin raba kawunan al’ummar ƙasar nan
IBB ya faɗi haka ne a yayin da ya amshi baƙuncin wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP. Inda ya buƙaci da su kasance masu mayar da hankali wurin yin siyasa mai tsafta, ba wacce za ta raba kawunan al’umma ba.
Jaridar LEADERSHIP A Yau ta bankaɗo cewa, wannan ziyara ce da neman iri, wanda wasu ƙusoshin jam’iyyar suka ziyarci IBB domin neman tallafinsa ga takarar Farfesa Tunde Adeniran, wanda ke muradin kujerar shugabancin jam’iyyar PDP ta ƙasa.
Cikin ‘yan tawagar da suka kai wannan ziyarar sun haɗa da Farfesa Jerry Gana, Tsohon gwamnan Jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau, Sanata Mantu, Tsohon Ministan Mata, Hajiya Zainab Maina, Hajiya Inna Ciroma da Alhaji Shehu Gabam.