Daga Rabiu Ali Indabawa
An cafke wata mata mai ‘ya’ya uku da aka mai suna Justina Eje bisa zargin dabawa mijinta wuka har lahira a yankin Ikorodu da ke Jihar Legas.
Matar mai shekaru 28 da haihuwa ta dabawa mijinta marigayi Edwin Anduaka wuka a lokacin da suke rikicin cikin gida.
Wacce ake zargin, da kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Legas, Hakeem Odumosu, ya gabatar da ita a gaban manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Ikeja, ta ce ta rabu da mijinta na wani dan lokaci.
Da take bayar da labarin yadda wannan mummunan lamari ya faru, Ta ce; “Mijina da ya rasu ya zo gidana a Ikorodu a waccan rana mai wahala. Yayin da yake cikin gidana, ya so ya karbar min sarka da wani kyalle. Daga baya muka fara rigima, na yi kokarin kwantar masa da hankali amma ya ki.
“Har Ya tafi amma daga baya ya dawo ya same ni a wurin kasuwancina, washe gari.
Ya ce yana son tattara kayan ‘ya’yan amma na fada masa za su tafi makaranta. Na roke shi.
“Duk wannan lokacin ina rike da wuka sai ya fara dukana. Abun takaici, wukar da take hannuna da ita da ita na huda cikinsa sai ya fadi kasa. An garzaya da shi asibiti inda aka tabbatar da mutuwarsa.”