CRI Hausa" />

Uwargidan Shugaban Sin Ta Tura Wasika Zuwa Makarantar Burg Gymnasium Ta Jamus

Uwargidan shugaban kasar Sin Peng Liyuan, ta aike da wata wasika ga malamai da daliban makarantar sakandare ta Burg Gymnasium ta kasar Jamus a ranar Talata, tana mai karfafa musu gwiwar ba da gudunmuwar karfafa abota tsakanin al’ummomin Sin da Jamus.

Peng Liyuan, wadda ta ce ta kalli bidiyon da wasu daliban makarantar hudu suka rera wata wakar Sinanci ta After the Pandemic, wato bayan annobar, ta ce sun bayyana kyakkyawar fata na marawa jama’ar dukkan kasashe baya wajen shawo kan cutar cikin gajeren lokaci.
Ta kuma tuna cewa, shekara guda ke nan da daliban suka marawa Sin baya a yakin da ta yi da annobar ta hanyar rera waka mai taken “Let the World Filled with Love”, wanda ya bayyana abotarsu ga Sinawa.
Ta kara da cewa, annobar na ci gaba da addabar duniya, don haka ta damu da lafiyar daliban, tana mai fatan su da iyalansu, za su dauki ingantattun matakan kandagarkin cutar.
Uwargidan ta shugaban kasar Sin, ta yi ammana cewa, an kusa samun nasara. Kuma za a dakile cutar muddun jama’ar dukkan kasashe suka hada hannu wajen yakarta. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CRI Hausa)

Exit mobile version