Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Remi Tinubu, ta ziyarci Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, da matarsa, Hajiya Hadiza, domin jajanta musu kan rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Maryam Namadi, da ɗansa, Abdulwahab.
Uwargidan Shugaban Ƙasa, tare da Uwargidan Mataimakin Shugaban Ƙasa, Hajiya Nana Shettima, da Uwargidan Kakakin Majalisar Wakilai, Hajiya Fatima Abbas, sun nuna alhininsu, inda ta jaddada cewa rayuwa da mutuwa suna hannun Allah.
- Karo Na 35 Ne Ministan Harkokin Wajen Sin Ya Kammala Ziyararsa Ta Farko A Kowace Shekara A Afirka Cikin Nasara
- Ya Kamata Senegal Ta Dauki Kasar Sin A Matsayin Abin Koyi Wajen Samun Ci Gaba
Gwamna Namadi ya gode wa Uwargidan Shugaban Ƙasa bisa ziyarar ta’aziyyar.
Ya bayyana cewa rasuwar mahaifiyarsa da ɗansa ƙaddara ce daga Allah da ba za a iya yin komai a kai ba.
Hajiya Maryam Namadi ta rasu a ranar 25 ga watan Disamba, 2024, bayan jinya, yayin da Abdulwahab, mai shekara 24, ya rasu a hatsarin mota a ranar 26 ga watan Disamba, 2024.
An yi wa iyalan gwamnan addu’o’i da jihar yayin ziyarar.