Van Dijk Ya Fara Buga Wasa A Liverpool Da Kafar Dama

Sabon dan wasan Liverpool, Birgil ban Dijk ya fara wasansa a Liverpool da sa’a bayan da ta sayo shi a kan fam miliyan 75 daga Southampton, inda a kusan lokacin tashi ya taimaki sabuwar kungiyar tasa da cin da ta doke Eberton 2-1 a wasan hamayya na zagaye na uku na kofin FA.

A fafatawar da aka yi a gidan Liverpool Anfield, kusan Everton na kan hanyar kai wasan karo na gaba a gidanta Goodison Park, kafin mai tsaron ragar bakin Jordan Pickford ya yi kuskuren fahimtar kwanar da aka dauko ya bari Ban Dijk, ya ci shi da ka saura minti shida lokaci ya cika.

Kwallon ta biyu wadda dan bayan mafi tsada, wanda ba a taba kashe kudi mai yawa aka sayo wani dan baya ba a duniya, ya ci ita ba wa Liberpool kaiwa zagaye na hudu na gasar ta cin kofin kalubale na FA.

Gylfi Sigurdsson ne ya farke wa Everton a minti na 67, bayan da tun da farko James Milner ya ci wa Liberpool da fanareti, minti 10 kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Alkalin wasa Bobby Madley wanda ya yi faman gaske a alkalancin wasan na hamayya kamar yadda daman aka saba yi a karawar, ya ba wa Liberpool fanareti ne sakamakon ketar da Mason Holgate ya yi wa Adam Lallana.

Liberpool ta yi wasan ne ba tare da dan gabanta ba, gwarzon dan kwallon kafar Afirka na Caf na 2017, Mohamed Salah, wanda yake jinya, da kuma gwanin dan wasanta na tsakiya Philippe Coutinho, wanda yakoma Barcelona a kan fam miliyan 140.

Kociyan Liberpool Jurgen Klopp bai bata lokaci ba wajen fara amfani da sabon dan wasansa na baya Ban Dijk, bayan da suka siyo shi daga Southampton – sai dai dan wasan na Holland mai shekara 26 a gaba a fara aikinsa, dacin kwallo din ta biyu, wadda ta kai su zuwa mataki na gaba a gasar ta kofin FA.

A wasanni na gaba dukkanin kungiyoyin biyu za su fafata ne a gasar firimiya, inda Everton za ta je gidan Tottenham ranar Asabar, 13 ga watan Janairu da karfe 6:30 na yamma agogon Najeriya.

Ita kuwa Liverpool sai washe-gari ne (Lahadi) za ta karbi bakuncin jagora a gasar ta firimiya Manchester City da karfe 5:00 na yamma agogon Najeriya.

Exit mobile version