Abba Ibrahim Wada" />

Van Dijk Yafi Messi Da Ronaldo Kokari –Van Persie

Tsohon dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Arsenal da Manchester United da Feyernood, Robin Ban Persie, ya bayyana cewa dan wasan kasarsa, Birgil Ban Dijk ya fi Messi da Ronaldo kokari a kakar wasan data gabata duba da irin kokarin da yayi.

Dan wasan Liverpool, Birgil ban Dirk shi ne ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na nahiyar Turai na bana bayan da ya taimakawa Liverpool ta doke Tottenham a wasan karshe a gasar cin kofin Zakarun Turai da aka kammala.

Ban Dijk mai shekara 28 ya yi nasara ne a kan shahararrun ‘yan kwallon duniya guda biyu, Lionel Messi na Barcelona da tsohon dan wasan Real Madrid, Cristiano Ronaldo mai buga wasa a Juventus.

Dan wasan ya zama kashin bayan Liverpool tun lokacin da ya koma Anfield da buga wasa daga Southampton a Janairun shekara ta 2018 kan fam miliyan 75 a matsayin dan wasan baya mafi tsada a lokacin.

Ban Dijk dan kwallon tawagar Netherlands ya taimakawa kasarsa ta kai wasan karshe a gasar cin kofin UEFA Nations League a bana, inda ta yi rashin nasara a wasan karshe a hannun Portugal mai masaukin baki.

Sai dai Ban Persie, wanda ya bugawa kasar Holland wasanni a baya ya  bayyana cewa irin kokarin da Ban Dijk yayi a matsayinsa na dan baya shine zaisa yafi Ronaldo da Messi kuma ya lashe kofin nahiyar turai wanda yana da babbar daraja a duniya.

Ya cigaba da cewa banda kofin zakarun turai daya taimaka Liverpool ta lashe ya kuma taimakawa kungiyar ta kammala kakar wasan firimiya a mataki na biyu kuma a wannan shekarar ma sune akan gaba akan teburin firimiyar.

Exit mobile version