Connect with us

WASANNI

Verdy Zai Maye Gurbin Torres A Atletico Madrid

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid ta kasar Sipaniya ta bayyana dan wasa Jermy Verdy a matsayin wanda zai maye gurbin dan wasan kungiyar da zai bar kungiyar, Fernando Torres a karshen kaka.

Kungiyar kwallon kafa ta Atletico, wadda ta lashe kofin Europa a satin daya gabata ta bayyana aniyarta na siyan Verdy da zarar Torres yabar kungiyar sannan kuma kungiyar tana shirin siyar da Antonio Griezman.

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ce dai take zawarcin Griezman wanda ake saran zai bar kungiyar a kakar wasannan bayan daya bayyana aniyarsa ta barin kungiyar domin zuwa babbar kungiya.

Sai dai a kwanakin baya kungiyar kwallon kafa ta Atletico ta bayyana cewa bazata siyar da dan wasan nata ba ga Barcelona saboda a cewarta Barcelona tana bin dan wasan ta bayan gida tana tattaunawa dashi.

Shugaban gudanarwar kungiyar ta Barcelona dai ya bayyana cewa a kwanakin baya sun tattauna da dan wasa Griezman inda ya ce suna son siyan dan wasan na gaba dan asalin kasar Faransa wanda ya koma Atletico din daga Real Sociedad.

Verdy ya zura kwallaye 23 a wannan kakar a kungiyarsa ta Leceister City da kasar Ingila sannan kuma Ingila ta gayya ce shi zuwa gasar cin kofin duniya wanda za’a fafata a kasar Rasha a wata mai kamawa.

A shekarar da ta gabata ne dai dan wasan yaki amincewa da komawa Arsenal duk da cewa kungiyar ta kai tayin kudi mai tsoka ga kungiyar Leceister City.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: