Vidic Ya Na Son Ya Zama Kociyan Manchester United

Tsohon dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Nemanja Vidic, ya bayyana cewa nan gaba kadan ya na son watarana a ce shine kociyan kungiyar domin ya kammala ciki burinsa.
Vidic, wanda yayi ritaya daga buga kwallo shekaru biyu da suka gabata a yanzu yana sharhin wasan kwallon kafa ne a gidajen talabijin kuma har yanzu dai bai koma harkokin kwallon kafa ba kamar da.
Tsohon dan wasan wanda dan asalin kasar Serbia ne ya bayyana burinsa na koyar da kungiyar ne domin fitar da kungiyar daga halin da take ciki na rashin tabbas tun bayan da tsohon kociyan kungiyar Sir Alex Ferguson yayi ritaya daga koyar da kungiyar.
“Idan kana kallon Manchester United a yanzu bazaka hada tad a yadda take ba a lokacin Sir Alex Ferguson saboda komai ya canja a kungiyar kuma magoya bayan kungiyar b ayadda sukeso suke gani ba.
Yaci gaba da cewa “Amma zamu yarda cewa yanzu kungiyar tana samun cigaba a hankali ba kamar lokacin baya ba saboda hakane ma nakeson zama kociyan kungiyar anan gaba domin dawo da komai yadda yake.
Vidic dai ya buga wasanni 300 a Manchester United kuma ya zura kwallaye da dama sannan ya lashe kofn firimiya guda biyar da gasar zakarun turai guda daya da kuma gasar Lig Cup wadda ya lashes au uku.

Exit mobile version