Connect with us

HAYAKI

Wa Zan Aura? (2)

Published

on

“Idan ka yi kuskuren auren mace, wadda ba nagartacciya ba. Idan kika yi kuskuren auren namiji. To a rayuwarka ka sami wani tabo, da yana da wuya ka iya warkewa daga wannan tabon. Kin sami tabo, tabon da yana da wahala ki iya warkewa daga wannan tabo din.”

 

Sheikh Guruntum

A makon da ya gabata mun fara bayani game da yadda malamai suke kwatanta abokan zaman aure da riguna. Bisa la’akari da suka yi da ayar nan da take cewa su (mata) sutura ne gare ku, kuma ku ma (mazan) sutura ce gare su.

Yanzu za mu fara da misalin rigunan, kamar yadda muka alkauranta.

 

Ire-iren Riguna

Sanin dukkanninmu ne cewa, sau da yawa mukan ce, mun fi son mu yi auren-jari. Wato mutum ya auro wata mai kudi ko ‘yar gidan wani hamshakin mai kudi, alhali shi yana talaka fitik. Wai saboda ta dalilin haduwar tasu, ko dai  shi ma a buda mar hanyar, wato a sa shi a wani wuri da zai rika samun kudin, ko ma a ba shi jari yana zaune. Ko kuma ma dai idan duk hakan ta ki, ko damfarar ta ya yi, ta hanyar shiraya wata dabarar da dolenta ta sakar masa kudi. Wannan dabi’a kuma ba wai ga mazan kawai ta kebantu ba. Haka su ma matan kan yi.  Sau da dama za ka kwashe dogon lokaci kana son wata yarinyar amma da zarar wanda ya fi ka numfashi ya zo, kai da kanka in kana son ka tsira da ragowar mutumcinka za ka ja jiki. Kuma yawanci ba su ma cika damuwa da hali ko dabi’arsa ba. Wata budurwa ta taba ce min:

“Ni fa a wurina ba wani abin damuwa ba ne wai don namiji ya zazzage ni. Idan dai har in ya gama zan je in kunna AC in bude firji in dau lemo mai sanyi in sha. In na gama in koma kan tattausan gado in kwanta!”

Wannan yana nuna watakila ba ta da wani zabi fiye da ta sami mutum mai hannu da shuni. Shekarun da muka yi maganar da ita suna da yawa, kuma har lokacin da nake wannan rubutun tana nan tana ta jira.

Mutum yakan auri Uniform, wato ita ce ‘yar gidan wani mai mulki, wadda idan ka aure ta, tamkar ka sanya wani inifom ne wanda in ba dan shi ba ba ka isa ka iya samun damar shiga wani wurin ba. Kamar dai yadda mutum yana matsayin dan talaka, zai iya samun damar shiga wurin da shugaban kasa ko gwamna ko kuma wani babban mai mulki yake, kawai saboda yana sanye da uniform din aikinsa na soja ko dansanda da dangoginsu.  Haka nan mutumin da zai auri ‘yar gidan wani hamsakin mai kudi,  wanda za kan iya kwatanta shi a matsayin wanda shi ma ya sa inifom ta wata sigar. Tun da ta dalilinta zai iya samun uzurin shiga wasu wuraren wanda ba don shi sirikin wane ba ne, bai isa ya doshi wurin ba. Ko kuwa ka kwatanta ta da matsayin babbar riga a wurinsa. Kamar dai yadda yanyin babbar rigar da ta sha aiki take. Duk lokacin da mutum ya sa ta, za ka taras daga zahirin abin da idonka zai gani dai kawai ba shi da wata matsala. Haka macen ma.  Da  gaske ne za ta iya zama sanadiyyar rufe mar dukkan wata kafa ta kananun matsaloli, wadanda a da can watakila sun sha mar kai. Kuma za ka ga alamar babu wata matsala daga jikinsa. Kamar dai yadda idan mutum ya sanya rigar a jikinsa za ta kare mar jikinsa kuma a gan shi fes-fes (daga abin da mutane za su iya gani a ido). Haka kuma abin yake ga matan da suke aurar manyan mazaje masu arziki ko mukamin, bisa ga wannan dalilan.

Abu ne mai kyau, a ce ka samu canji a rayuwa. Sai dai kuma da yake muna maganar aure ne, ba wannan ne babban abin dubawa ba. Domin a irin wannan hadin a mafi yawan lokaci gagarumar rashin jituwa ce kan biyo baya, har ma dai wani lokacin mutum ya yi da-ka-ce.  Domin zai yi matukar wahala ka iya samun cikakken ikon sarrafa ta, kamar yadda sauran maza kan iya juya matansu. Za ka fadi wani abu da ya dace a yi, wanda ba lallai ne ta yi ba idan har bai yi daidai da ra’ayinta ba,  ko kuma idan ta ga za ta takura kanta, ko ma dai abu ne da idan kawaye suka gani za su ce ta dauki miji uba. Kuma kasancewarku wadanda kuka taso a gidaje masu mabambantan tarbiyya, za ka taras a mafiya yawan lokuta yadda kuke kallon abubuwa ba daya ba ne. Abubuwa da dama da kake kallo a matsayin wayewa,  ita kauyenci ne a wurinta, domin ba haka ta saba ganinsu ba.

Sau da dama za ka ba ta umarni ta fake da wani abu ta ki bi. Domin Shaidan yana yana tuna mata cewa ita fa taimaka ma kawai ta yi ta aure ka. To a kan me kuma kai za ka zo ka takura mata, don ta zo taimako, maimakon ma kullum ka rika yi mata hidindimun kana yi mata godiya duk da haka. Kai kuma a lokacin abin da zai rika hargutsa ka, shi ne bayan kana ganin tana karkashinka, don haka dole ta bi umarninka, kana kuma gani tsoron kar ka bari ta raina ka saboda tana da kudi. A lokaci guda kuma kana tsoron kar dangi da abokanka su fahimci ta raina ka, a rika yamadidi da kai, a ace maka mijin-ta-ce. Sai ka taras duk giraman kan duniya an dauko shi an shirga maka a ka.  Yayin da ita ma take nade da irin nata rawanin.

A hannu guda kuma,  a can baya mun yi maganar cewa, aure ba wai masalahar kanka kadai ce a bar dubawa ba. Idan aka zo maganar mu’amularsu da danginka, za ka taras daidai ne wadda ba za ka ji dangin suna kukan ta cika rainin wayo ba. Domin idan mai jin izzar kudin ce, za ka taras ba su ishe ta kallo ba. Idan kuwa ba mai kirki ba ce ma wannan kuma ba wai  kannenka ko yayyinka ba, sau da dama har iyayenka sai sun kaurace wa inda kuke, gudun kallon karan-kada-miyar da take yi musu.  Haka nan ma abokanka kan iya fuskantar irin wannan matsalar.  Wannan idan burinka ya cika an sakar maka kudin kenan. Idan kuwa aka yi rashin gam-da-katar ba a sakar maka kudin ba, labarin zai fi haka rashin dadin ji kenan.

Abin da kai ba ka sani ba shi ne, a irin wannan yanayi, ba wai kai kadai ko wanda yake a jikinka ba, dukkan mutanen da ke kusa da kai ma, za su iya fahimtar cewa kana cikin wani yanayi, kamar dai yadda mutumin da ya sanya kambarereyar riga kuma ana cikin lokacin matsanancin zafi yakan shiga. Lallai da zarar mai hankali ya kalle ka, zai iya fahimtar akwai wani abu.

Za mu dora, in sha Allahu.

 
Advertisement

labarai