Connect with us

Uncategorized

Wa Zan Aura?

Published

on

“Idan ka yi kuskuren zabin matar da za ka aura. Idan kika yi kuskuren zabin mijin da za ki aura.
Za ka yi nadama. Nadamar da ba za ta amfane ka ba.
Za ki yi nadama. Nadamar da ba za ta amfane ki ba.
“Idan kika yi kuskure. Idan ka yi kuskure. Kika zabi miji, wajen (akasin) shawarin Annabi SAW. Idan ka zabi mace, wajen shawarin Annabi SAW.
Wallahi za ka koka! Wallahi za ki koka!” -Sheikh Guruntum
Mutumin da ba shi da aure a kodayaushe yana kallon kansa ne a matsayin wani mutum mai karancin farin cikin rayuwa, yayin da ya kwatanta kansa da masu aure. Kuma wannan shi ne tunanin mafi yawan marasa aure. Amma a wata kasida da Tim Urban ya gabatar ya tabbatar da cewa, mutum maras aure yana tsakiyar masu aure biyu ne. Wato wasu masu auren sun fi shi farin cikin rayuwa, yayin da shi ma ya fi wasu da dama.
Tim yana da ra’ayin cewa, da gaske ne ana samun nutsuwa da farin ciki mai yawan gaske a gidajen aure. To amma hakan ba wai yana nufin dukkannin gidajen auren ne suke da haka ba. Wato ba kowadanne ma’auratan ne suke yin wannan gam da katar din ba. domin wasu dunbun gidajen suna nan su kuma suna fama da dumbun bakin ciki da kuncin rayuwa, sakamakon auren. Har ma dai da yawa daga cikin ma’auratan suna muradin ina ma dai a ce su ne wancan da bai yi auren ba! wannan kuwa duk yana faruwa ne sakamakon zabin aboki ko abokiyar zaman auren. Idan kuwa haka ne, to ashe watakila babu wani abu da ya kai zabin abokin zaman muhimmanci a sha’anin aure. Don haka dolenmu ne mu yi mar karatun ta nutsu.
Zaben abokin zama ba wai yana nufin zabar wadda ko wanda yake burge ki a matsayin da kike a yanzu ba ne. A’a, a takaice akwai bukatar bayan ka duba masalahar kanka. Ka duba masalahar iyaye da danginka, wa kake shirin kawo musu cikinsu? Shin za su yi alfahari da kasancewar wannan a matsayin da ko ‘yarsu? Masalahar ‘ya’yan da za a iya samu a wannan auren. Wadannan fannoni uku suna da muhimmanci matuka, yayin zaben abokin zama. Wato kai karan kanka, da iyaye ko danginka da kuma zuri’ar da ake sa ran samu sakamakon auren. Don haka za mu taba kowane bangare, bisa gwargwadon iko, in sha Allahu.
Bai kamata ka auri mace ba face ka tabbata cewa kana so ka haifi ‘ya irinta sak. Haka kuma ke ma bai kamata ki auri kowane mutum ba sai dai in a ranki kin tabbata samun da irinsa sak a wurinki ba matsala ba ne.

Me Ya Kamata Ka Yi La’akari Da Shi Yayin Zaben Abokiyar Zama?
A karan-kanka: Babu shakka akwai abubuwa da dama da suka kamata mu rika dubawa yayin da muka tashi yin wannan muhimmin zabe, bisa la’akari da addini da zamani har ma da al’ada da muhalli da makamantansu.
Daga cikin abubuwan da su ka kamata mu dauka su zame mana ma’auni na zaben akwai Ayar nan da take siffanta ma’aurata da sutura ga junansu. Wato “Hunna libasin lakum wa antum libasin lahun.” Shin mene ne hikimar siffanta ma’auratan da matsayin SUTURA ga juna?
A kalla dai, ko ba komai dukkanmu za mu iya yarda cewa, sutura ko tufafi su ne mafi girman abin da mutum ke suturta kansa da shi. Yake rufe tsiraici, yake ado, yake kare sanyi ko zafi. Sannan kuma yanayin tufar yana da tasiri game da darajar mutumin a idon jama’a. kamar kuma yadda addini ma yana da ruwa da tsaki game da yanayin sa tufafinka. Wannan kuma shi ya sa za ka taras kowa yana da zabinsa game da tufafi. Kuma kowa akwai dalilan da suka sa yake nasa zaben.
To tunda Kur’ani ya kwatanta abokin zama da tufafi, bari mu dauke shi a matsayin RIGA. Misali, za mu iya cewa kamar yadda riguna suke iri-iri haka ma mata suke. Wato akwai Babbar-riga, akwai Jamfa, akwai ‘Yar-shara, akwai Tazarce, akwai Shat, har ma da Singileti da dangoginsu. Akwai kuma Rigar-sanyi da ta zafi da Uniform da Khaki da sauransu. Don haka muhimmin abu da ya kamata mu fara la’akari da shi yayin zaben rigar da za mu sa, shi ne yanayinmu. Wato abin da ya hada da yanayin girman jikinmu (tsayi ko kauri) da kuma yanayin da ake ciki (zafi ko sanyi).
Yana da kyau matuka ka duba wace rika ce idan ka saka ta za ta yi maka daidai. Ta yi maka cif-cif a jiki, ba tare da ta yi yawa, kana tafiya buguzum-buguzum a ciki ba. Ba kuma tare da ta dangale ma, ana gano wasu sassan jikinka a waje ba. Ko kuma kamar raga, ana hangen surorin jikinka daga nesa. Kuma kar ka manta da canje-canjen yanayi. Ka zabi rigar da za ka iya sawa a kowane irin yanayi. Idan ka zabi rigar sanyi kuma idan lokacin zafi ya zo sai ka gane kurenka. Haka in ka zabi singileti, idan lokacin sanyi ya zo sai ka kusa mutuwa! Kar kuma ka kuskura ka zabi uniform, domin idan ka lura, masu aiki da shi ma suna zuwa gida shi suke fara cirewa.
Kamata yai ka tsaya ka duba da kyau, ka zabi rigar da za ta yi ma cif-cif, kuma wadda a kowane lokaci ba za ta gundire ka ba. Kar ka manta, idan fa riga ba ta yi maka daidai ba, duk mutumin da ya kalle ka ma zai iya ganewa.
Abubuwan da suka kamata a duba a nan sun wuce suna ko kyan rigar kawai. Dole ne kowane mutum sawa’un mace ce ko namiji, kamar yadda idan ka tashi dinkin riga sai ka tsaya ka dubi launin atamfar ko yadin, shin kalar za ta dace da kai? Kuma sai ka zabi Telan da kake tunanin kwararre ne, wanda idan ya yi maka dinkin kai da kanka sai ka ji ka fi nutsuwa yayin da ka saka rigar a jikinka. Kuma kana la’akari da yanayin jikinka, wato girman jikinka. Misali, idan kai siriri ne ba za ka tunkari zumbuda rigar da lukutin mutum zai sa ba, domin sai a gan ka da ban a gefe guda, rigar ma da ban iska tana falfala ta. Haka kuma idan kana da kauri ba za ka zabi rigar da aka dinka don siririn mutum ba. Domin watakila kai da kanka idan ka saka ta daga gida ka ji kana kunyar fitowa waje mutane su gan ka. Saboda yadda za ta yi maka fikil a jiki. Amma kuma abin sha’awar shi ne, wadda kai ka sa ta yi maka yawan ko ta yi maka kadan din ita ce kuma daidai da wani!
Da sannu za mu kawo misalan rigunan, ta hanyar da za mu fi fahimta, in sha Allahu.
Advertisement

labarai