WA’AZIN KIRISTA: Matsayin Kirista A Duniya Tamkar Gishiri Ne A Abinci

Tare Da Fasto Yohanna Y.D. Buru  0806 871 8181 yyohanna@gmail.com

Gaisuwar ƙauna a cikin sunan Yesu Almasihu. Yau za mu karkata jawabinmu ne zuwa kan maganar ‘Matsayin Kirista A Duniya.’

Karatunmu na samuwa a cikin Littafin Matta 5:13-16. Ɓ13 “Ku ne gishirin duniya: amma idan gishiri ya rabu da zaƙinsa, da me zai gyaru? Nan gaba ba shi da amfani ga komai ba, sai a yas, a tattake ƙarƙashin sawun mutane.

Ɓ14 “Kune hasken duniya. Birnin da me kafe bisa tudu ba shi biyuwa.

Ɓ15 “Kuma ba a kan kunna fitila a sa ta ƙarƙashi akushi ba, amma bisa tabur; sai ta haskaka ma dukan waɗanda ke cikin gida.”

Ɓ16 “Haka nan ku kuma ku bari haskenku shi haskaka a gaban mutane, domin su ga ayyukanku masu kyau, su girmama Ubanku wanda ke sama.”

Tare da yardar Allah, za mu ɗauki lokaci muna fassarar waɗanan ayoyin, domin mu fahimci mene ne Yesu Almasihu ke nufi da wannan koyarwar. Yesu ya yi wannan koyarwar akan sanannen alama ne, wato akan gishiri da fitila. Masu jin sa a wannan lokacin, suna sane da mene ne gishiri ko fitila, amma ba su san da ma’anarsu ba a cikin koiyaruwar ba.

Kafin Yesu ya kai ga wannan koyaruwar sai da ya ɗauki lokaci yana koyarwa akan halayen da ya kamata a sami Kiristoci da su kafin su zama magadan mulkin Allah, (Matta 5:1-12). Sai ya kai ƙololuwar koyarwar sa shi ne a (Matta5:13-16), a nan ya buƙaci Kiristoci da su bar kyawawan halayansu, ya bayyana ga duniya kamar gishiri da kuma fitila suke, domin mutanen duniya su shaida cewa su Kiristoci daban ne suke da kowanne irin mutum. Sai Yesu ya ce wa Almajiransa da kuma masu sauraronsa da cewa:

Ɓ13 “Ku ne gishirin duniya: amma idan gishiri ya rabu da zaƙinsa, da me zai gyaru? Nan gaba ba shi da amfani ga komai ba, sai a yaswa, a tattake ƙarƙashin sawun mutane.”

Gishiri wata sananniyar alama ce kuma sanannen sinadari ne da ake amfani a kullayaumin a dahuwa ko ayyukan haɗayu a Haikalin Ubangiji da wasu aikace- aikace. Wato gishiri ga masu sauraronsa a wannan lokaci wata sanannen abu ce da kusan kowa ya sani sosai.

Gishiri da Yesu ke magana, iri wani gishiri ne da ana amfani da shi a ƙasar Isra’ila, da ana samunsa a Dead Sea, wanda in an bar shi a rana tabbatace  zai lalace.

Amma a nan Yesu Almasihu na so ya yi amfani da gishiri da ke sananne ya yi masu koyaruwar akan abin da ke na Ruhaniya ne ko kuwa yadda matsayi ko halayyar Kirista da ke ganuwa ga waɗanda ba Kiristoci ba ne.

Yesu ya ce masu, “ku ne gishirin duniya…” Bisa ga ganewar Malaman addinin Kirista, sun tabbatar mana da cewa babu wani Malamin addini da ya taɓa baiwa mabiyansa ko Almajiransa suna ko kiransu “gishirin duniya.” Domin a Gabas ta Tsakiya ta gefen Turawan Yamma, babu ko mutum guda da an taɓa ba shi ko su, “gishirin duniya,” duk da darajar da ake ganin ta, ko ta wurin amfani a kowane fanni.

Kyau gishiri ko kuwa kyawawan abubuwan da ke ƙunshe a cikin gishiri na da yawa sosai. A cikin kyawawan abubuwan da ke ƙunshe ne ya sa Yesu Almasihu ya kira Almajiransa, masu sauraransa a lokacin da kuma Kiristoci da cewa su ne gishirin duniya.

Kyawawan abubuwan da ke cikin gishiri na nan a cikin kowanne cikakken Kirista, shi ya sa Yesu Almasihu ya ce su Kiristoci su ne gishirin duniya. Amma mene ne kyawawan abubuwan da ke cikin gishiri da Yesu ya alaƙanta Kiristoci da shi? Abubuwan da ke ƙunshe a cikin gishiri su ne:

  1. Gishiri na da ɗanɗano, ko kuma gishiri na fitar da ɗanɗano abinci ya yi daɗi.
  2. Gishiri sinadarin haɗa kowane abu a cikin abinci domin ya yi daɗi
  3. Gishiri na da sinadarin da ke ƙare abinci lalacewa ko ruɓewa.
  4. Gishiri ta kan tsarkake abu daga lalacewa.

 

Waɗanan kyawawan abubuwan da ke ƙunshe a cikin gishiri suna cikin Kirista da ya kamata ya zama missali a duniya.

Ga fassara ko ma’anan waɗanan abubuwa guda huɗu:

  1. Ta wurin rayuwar da kyawawan halayen Kirista ya kan sa duniya ta yi daɗin zama ga kowanne irin mutum ko waɗanda ba Kirista ba. Irin rayuwar Kirista ya kamata ta zama da sha’awa ga kowane irin mutum, domin cikakken Kirista ya kamata ya zama daban. Kuma ya kamata rayuwar Kirista ta zama missali ga kowanne irin mutum, domin shi ne gishirin zaman duniya. Kirista zai sa duniya ta yi daɗin zama ga kowa da kowa.
  2. Gishiri sinadarin haɗa abubuwa a cikin abinci domin ya yi daɗi. Ya kamata Kirista ne ko Kiristoci ne su zama masu haɗa kan jama’a domin a sami zaman lafiya a duniya. Wato matsayin Kirista a duniya shi ne ya zama mai haɗa kan jama’a a ko’ina a kuma kowanne lokaci, kamar yadda gishiri na haɗa komai da komai a cikin abinci har ya haɗu daɗi domin ci.
  3. Ya kamata Kiristoci su zama masu kare duniya daga lalacewa. Kiristoci, su ne gishirin duniya da za su ƙari duniya daga lalacewa, domin sun ilmantu akan maganar Allah, wato suna da Kalmar gaskiya.

Yesu ya ce masu:

“Ku a san gaskiya kuma, gaskiya kuwa za ta ‘yantar da Ku” (Yohanna 8:32).

In Kiristoci masana gaskiya ne, kuma gaskiya ita ce kaɗai za ta ’yantar da su, to ashe Kiristoci ne za su iya hana duniya daga lalacewa.

  1. Gishiri ya kan tsarkake abubuwa daga lalacewa. In Kirista zai yi rayuwa bisa ga koyarwar Littafi Mai tsarki, to tabbas ne ya yi zaman tsarki domin a tsarkake duniya daga illolin zunubai. Matuƙar Kirista na da tsarki zai iya koyar wa mutanen duniya zaman tsarki, har duniya ta tsarkaku daga illolin zunubai domin salama da ci gaban al’umma.

A taƙaice, kyawawan halayen Kiristoci misali ne ga duniya, domin waɗanan kyawawan halayen ne ya bambanta Kirista da kowanne irin mutum a duniya.

Yesu ya ci gaba da maganarsa akan tambaya cewa: “…amma idan gishiri ya rabu da zaƙinsa, da me zai gyaru?

Ma’anar wannan tambayar, duk kyawawan halayen da Kirista ke da su domin ingancin zaman duniya, matuƙar ba shi da waɗanan kyawawan halayen, to ya zama kamar gishirin da ya rabu da zaƙinsa. Kuma gishirin da ya rabu da zaƙinsa ba ya da ko amfani. kuma in Kiristoci, sun rasa kyawawan halayen su, to ba za a sami haɗin kan jama’a ba, babu jin daɗin zama a duniya, duniya ta da tsarki da kuma duniya ba za ta lalacewa ba.

Yesu ya ƙarasa wannan ayar da cewa:  “….nan gaba ba shi da amfani ga komai ba, sai a yarwa, a tattake ƙarƙashi sawun mutane.”

Abubuwan da suka tabbatar wa duniya cewa mutum Kirista ne, to shi ne kyawawan halayen da suka bambanta shi da kowanne irin mutum. To, ga shi mutumin da ke iƙirari da cewa shi Kirista ne, sai ga shi ba shi da halayen da ya cancanci a ce ko a kira shi Kirista.

Kuma kamar yadda gishiri na da amfani ga abinci, haka ne Kirista na da amfani ga duniya. Abubuwan da suka sa gishiri ya zama gishiri in babu shi a cikinta, to ba gishiri ba ne. Haka ma, in abubuwan da ke cikin da suka mayar da Kirista, Kirista in babu su, to wannan mutumin ba Kirista ba ne.

Domin da haka Kiristan da ba cikaken Kirista ba, abubuwan da ke mayar da mutum Kirista babu a cikinsa. To ba Kirista ba ne komin kamarsa da Kirista, ba Kirista ba ne. Baicin haka, ya kamata kada a sa su a cikin lissafi akan cewa su Kiristoci ne.

Haka ma gishirin da zaƙinsa ya rabu, wato kyawunsa a zubar da shi ko a yas da shi, a tattake ƙarƙashin sawun mutane. Domin tsananin rashin amfanin gishiri, Yesu ya ce kyawunsa a yas da shi domin a tattake ƙarƙashi sawun mutane.

Wannan wani darasi ne ga kowanne Kirista. Matuƙar Kirista ya lalace ko ya rasa kyawawan halayen da aka san shi a matsayin Kirista, to ba shi da amfani, kamar gishirin da ya rabu da zaƙinsa, ya kuma zama marasa amfani. To kyawunsa, shi a zubar ko a yas da shi domin a tattake ƙarƙashi sawun mutane.

Yau waɗanda sunaiƙkirari da cewa su Kiristoci ne, amma sun rasa kyawawan halayen Kirista, tabbatacce ne ba su da kima ko daraja ko mutunci a gaban mutanen duniya. Shi ya sa Kirista na shan wulaƙanci a ko’ina a yau hannun mutanen duniya.

Mu na fata da cewa, Kiristoci za su gane daga wurin da suka kauce a hanyar Allah, su dawo kan hanya domin rahamar Allah da kuma jin ƙai na Ubangiji Allah shi tabbata akansu daga yanzun har abada-abadin Amin Thumma Amin.

 

Za mu ɗora daga nan mako mai zuwa. Shalom! Shalom!! Shalom!!!

 

 

Exit mobile version